Majalisar Wakilai ta janye ƙudirin ɗaure waɗanda suka ƙi rera sabon taken Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar Wakilan Nijeriya ta bayyana cewa an janye ƙudurin dokar da za ta hukunta ’yan Nijeriya da suka ƙi rera sabon taken ƙasa.

Daga cikin tanade-tanaden ƙudirin, akwai hukunta masu wulaƙanta alamomin ƙasar nan da kuma lalata wurin ibada a faɗin Nijeriya.

Majalisar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa shugaban majalisar da kansa ne ya bijiro da ƙudurin a ranar Talata , 23 Yuli, 2024, kuma tuni ya jawo Allah-wadai daga jama’ar ƙasa.

Majalisar ta ce, shugabanta ya zurfafa bincike domin gano ko ƙudurin zai yi daidai da cigaban ‘yan ƙasar nan domin tabbatar da nasarar bunƙasa Nijeriya.

Ta wallafa cewa, ƙasar nan ta bayyana dalilan janye dokar hukunta masu wulaƙanta taken ƙasar nan da sauran abubuwa, da lalata wuraren ibada.

Majalisar ta bayyana cewa shugabanta, Hon. Tajuddeen Abbas mai jin koken ‘yan ƙasar nan ne, kuma ba zai yi abin da zai takurawa kowa ba, musamman bayan shawarwari.

Mashawarcin shugaban majalisa, Musa Krishi ya ce Hon. Abbas ya tattauna da ƙusoshin ƙasar nan kuma ya amince da shawarar dakatar da ƙudurin dokar.

By ukarofi