Gwamnatin Tarayya na ƙara ƙaimi wajen ganin abinci ya wadata a faɗin ƙasar.
Jaridar Blueprint ta yi duba da irin shirin da gwamnati ta yi a baya da wanda take yi a yanzu domin ganin matsalar abinci ya ƙare a ƙasar, wanda in bamu manta ba, yunwa da rashin abinci na ɗaya daga cikin dalilan da suka janyo zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi.
A baya gwamnatin a cikin shirye-shiryen ta ba samar da iri mai kyau ga manoma da kuma sayar ma ma’aikatan gwamnati buhun shinkafa a kan N40,000.
Idan bamu manta ba, hukumar kwastom ta ƙasa ta janye haraji a kan wasu kayayyakin abinci da suka shagi dangin hatsi.
Wannan matakin kamar yadda ministan Kuɗi na ƙasa ya faɗa Wale Edun, an yi hakan ne domin kayan abinci su sauko da farashi.
Shima Shugaban Kwastom ya bayyana hakan da cewa, hukumar za ta yi bakin ƙoƙarin ta domin ganin wannan shirin yayi nasara. Duk da samun tsaiko da aka yi a watan da ya shuɗe.
Ministan Noma, Abubakar Kyari shima ya bayyana irin shirin da gwamnatin ke yi domin ganin abinci ya wadata a ƙasar. Ya faɗi shirin shugaban ƙasa na PASAP wanda an ƙirƙire shi ne domin kawo sauƙi ga lamarin noman abinci a ƙasar. Sai kuma shirin daidaita farashi da gwamnatin ta ƙirkiro, da kuma shirin noma da ya ƙunshi manyan kayan aiki.
Daga ƙarshe gwamnati ta shiga yarjejeniya da kamfanin John Deer Group wanda kamfani ne ƙarƙashin TATA wajen ganin a ƙera da kawo sabbin tarakata 10,000 daga yanzu zuwa shekara biyar.
