Majalisar Zartarwar Kano ta amince da biliyan N8.53 don ayyukan ci gaba

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta amince da kashe jimillar Naira biliyan 8.53 domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fannonin ababen more rayuwa, lafiya, ilimi, samar da ruwan sha da kuma jin daɗin al’umma a faɗin jihar.

An yanke wannan shawara ne a taron Majalisar Zartarwa na 37 da aka gudanar a ranar Alhamis, 16 ga Janairu, 2026, a Malam Aminu Kano House, Gidan Gwamna da ke Asokoro, Abuja.

Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala taron, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa ayyukan da aka amince da su sun shafi Ma’aikatun Gwamnati, Sassa da Hukumomi (MDAs) daban-daban, kuma an tsara su ne domin inganta hidimomi, tsaro da kuma bunƙ asa tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

A cewarsa, mafi girman kaso daga cikin kudaden da aka amince da su ya haɗ a da Naira biliyan 3.1 domin samar da sinadarin aluminium sulphate (alum) mara ƙarfe, don tace ruwan sha a faɗin jihar na tsawon watanni shida a shekarar 2026, ƙarƙashin Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.

Haka kuma, Majalisar ta amince da Naira biliyan 1.7 domin gina titin shafe-shafe sau biyu daga Chiromawa zuwa Garun Babba a ƙaramar Hukumar Garun Malam. An kuma amince da Naira miliyan 677.5 domin sake gina, gyarawa da farfado da Asibitin Janar na Rogo bayan gobarar da ta tashi a cikinsa.

Bugu da ƙari, an ware Naira miliyan 520 domin sayen na’urar CT Scan ga Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, yayin da aka amince da Naira miliyan 660.3 domin gina magudanan ruwa da shimfiɗa tayal (interlocking) a yankin Ayagi–Aisami, Unguwar Bakin Ruwa, a ƙaramar Hukumar Dala.

Sauran ayyukan da aka amince da su sun haɗ a da gina masaukin marayu a Cibiyar Kula da Yara ta Nassarawa, gyaran Makarantar Sakandiren ƙananan Dalibai ta Gwamnati (GJSS) Tatsawarki da ke Karamar Hukumar Kumbotso, da kuma biyan diyya ga gonakin noma da aikin gina ƙananan madatsun ruwa guda biyar ya shafa a wasu ƙananan hukumomi.

Haka zalika, Majalisar ta amince da gina Arewa Knot da kuma famfunan ruwa masu matakai da dama a yankunan Alfurƙan da Baban Gwari, tare da amincewa da biyan Naira miliyan 251.9 a matsayin diyya ga kadarorin da aikin gina titin zamani mai nisan kilomita biyar a ƙaramar Hukumar Bagwai ya shafa.

Dangane da batutuwan manufofi, Majalisar Zartarwa ta nuna matuƙar damuwa da alhini kan rasuwar wata mara lafiya a Cibiyar Urology ta Abubakar Imam, inda aka ruwaito cewa an bar almakashi a cikin cikinta yayin aikin tiyata. Majalisar ta yi kakkausar suka kan lamarin, tana mai bayyana shi a matsayin mummunar sakaci, tare da tabbatar wa al’umma cewa za a bi binciken da ake gudanarwa har zuwa ƙarshe.

Majalisar ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayiyar, tare da jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na kare rayuka da tabbatar da jin daɗin al’ummarta.

Haka kuma, Majalisar ta amince da muhimmancin aikin bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), tare da amincewa da bunƙasa Yankin Masana’antu na AKK da ke Tamburawa a matakai, inda mataki na farko zai mayar da hankali kan samar da muhimman ababen more rayuwa da shingayen tsaro.

Bugu da ƙari, Majalisar Zartarwar ta amince da cikakken gyara da inganta kayayyaki a sansanin horas da matasan NYSC da ke Karaye, domin magance matsalolin gine-gine da kuma inganta walwala, tsaro da jin daɗ in matasan da ke yi wa ƙ asa hidima a Jihar Kano.

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada ƙudirinta na amfani da albarkatu yadda ya kamata, tare da ci gaba da zuba jari a ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.

By ukarofi