Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina ta tallafa wa ‘ya’ya mata da kayan fara sana’o’i a jihar.
Yaran da suka kammala samun horan a cibiyoyi koyon sana’o’i guda 9 sun fito daga sassa daban-daban na jihar.
‘Yan matan sun koyi sana’ar ɗinki, saƙa,.yin takalma, gyaran kai da sana’ar noma da sauransu.
Bikin bada tallafin ya gudana a Centre kuma sashin kula da ilimin ‘ya’ya mata watau Department of Girl Child Education ƙarƙashin jagorancin babban daraktan Jamila Abdu Mani ta shirya.
A jawabinsa bayan da ya ƙaddamar da bada tallafin, Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana wannan shiri a matsayin ƙudirin gwamnatin sa ƙarfafa wa sana’o’i da kuma bunƙasa kasuwancan da tattalin arzikin jihar.
Ya bayyana cewa ka ba ‘ya’ya mata ilimi ka kuma tallafa masu tamkar ka taimaka wajan cigaban al’umma, gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da cewa kowace ɗiya mace Ilimi ta kuma yi amfani da shi wajen cigaban al’umma.
Gwamnan ya sanar da cewa gwamnati na shirin tallafi wasu ya’ya 14000 a faɗ in jihar nan bada jimawa ba.
Ya yi kira ga waɗ anda suka amfana da tallafi da suyi amfani da shi yadda ya dace, ya bayyana cewa gwamnati zata cigaba da ba mata horo da tallafin kudi da kuma kayan aiki don bunƙasa kasuwancan da tattalin arzikin jihar.
A nata jawabin babban daraktan sashin ilimin ‘ya’ya mata Hajiya Jamila Abdu Mani ya gargaɗ i waɗ anda suka amfana da tallafin da su guji karkatar ko dai da da kayayyakin wanda hakan a cewar ta kaman cin amana ne.
