Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Jakadiyar zaman lafiya ta garin Gama, Hajiya Suwaiba Muhammad ɗankabo, ta jinjinawa Dagacin Gama, Alhaji Rabi’u Isyaku, bisa irin rawar da ya taka wajen samar da haɗin kai, juriya da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin al’ummar yankin.
Hajiya Suwaiba ta bayyana hakan ne a yayin bikin cika shekaru 25 da naɗ a Alhaji Rabi’u Isyaku a matsayin Dagacin Garin Gama, wanda aka gudanar a makon jiya. Ta ce Gama gari ne da ya haɗa Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba, tare da mutane masu harsuna da ƙabilu daban-daban, amma duk da haka ana zaune lafiya da fahimtar juna, ta yadda ba a iya bambancewa a tsakanin al’ummar.
Ta bayyana cewa ta yi aiki a cikin garin Gama na tsawon shekaru biyar, kuma yana daga cikin garuruwan da take alfahari da su. A cewarta, Dagacin Gama shugaba ne mai jajircewa da hangen nesa, wanda ya fi mayar da hankali wajen ɗora matasa a kan tafarkin da ya dace tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Jakadiyar zaman lafiyar ta ƙara da cewa matan Gama da na Tagarji sun samu gagarumar nasara a fannin sana’o’i da zamantakewa. Ta ce an sami haɓakar sana’o’i, zaman lafiya a tsakanin iyalai, da kuma ƙarfafa gwiwar mata wajen dogaro da kai ba tare da jiran tallafin gwamnati ba.
A ƙarshe, Hajiya Suwaiba Muhammad ta yi kira ga al’ummar Gama da su ci gaba da bai wa Dagacin goyon baya da haɗin kai tare da yi masa addu’a, domin Allah ya ƙara ba shi ikon jan ragamar yankin cikin adalci da gaskiya. Ta kuma bayyana cewa a yayin taron, ita da mai ɗakinta sun sayi kalandar da aka ƙaddamar domin nuna goyon bayansu ga ci gaban yankin.
