Makarantar Nuru Raudatur Nabiyyu ta gudanar da saukar Alƙur’ani ta farko ga ɗalibai 40

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan Yaɗa Labarai, Malam Abdul’azeez Abdul’azeez, ya yaba da ƙoƙarin masu gudanar da Madarasatur Nuru Raudatur Nabiyyu Litahfizul ƙur’ani Wal-Darasatul Islamiyya, da ke Fagge, Kano, bisa irin gudubmawar da suke bayarwa wajen samar da ilimin addini da na Alƙur’ani ga yara da matasa.

Malam Abdul’azeez ya bayyana hakan ne a yayin bikin saukar Alƙur’ani ta farko da kuma taron karrama wasu fitattun mutane da suka taka rawa wajen tallafa wa ilimi da ci gaban makarantar, wanda aka gudanar ranar Asabar.

Ya ce irin waɗannan makarantu na da muhimmiyar rawa wajen samar da ilimi da tarbiyya nagari a cikin al’umma.

Saboda haka, ya yi kira ga iyaye da sauran al’umma da su ci gaba da tallafa wa makarantu irin wannan, yana mai sanar da bayar da gudunmawar Naira 250,000 domin tallafa wa makarantar.

Da yake jawabi, Shugaban Makarantar, Malam Magaji Ibrahim Abdullahi, ya ce wannan ce saukar Alƙur’ani ta farko da makarantar ta gudanar tun bayan kafa ta a shekarar 1435 bayan Hijira, wadda ta yi daidai da shekarar 2013.

Ya bayyana cewa makarantar ta fara ne da ɗalibi guda a cikin gida, kafin daga bisani ta bunƙasa ta koma cikakkiyar makaranta mai ɗimbin ɗalibai.

Ya ƙara da cewa, a lokacin zaman gida da aka yi sakamakon annobar Korona, adadin ɗaliban makarantar ya ƙaru sosai, inda suka kai kusan 1,000.

A cewarsa, a halin yanzu makarantar tana da ɗalibai da malamai masu yawa, duk da ƙalubalen da take fuskanta.

Malam Magaji ya bayyana cewa ɗalibai 40 ne suka kammala saukar Alƙur’ani a wannan karon, ciki har da mata 15 da maza 25.

Ya yaba da goyon bayan da makarantar ke samu daga iyayen ɗalibai, yana mai cewa haɗin kan iyaye na taimakawa wajen ci gaba da ayyukan makarantar duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Shugaban makarantar ya kuma bayyana cewa kusan mutane 70 ne aka karrama a wajen taron, ciki har da wasu daga cikin waɗanda suke raye da kuma waɗanda suka riga mu gidan gaskiya, bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban makarantar da ilimi.

Ya ce waɗanda aka karrama sun haɗa da malamai, ’yan siyasa, limamai, ladanan masallatai da sauran jiga-jigan al’umma.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai Farfesa Umar Sani Fagge, Alhaji Hamisu Danwawu da Alhaji Sagir Abba, tare da sauran masu ruwa da tsaki daga ƙaramar hukumar Fagge.

An gudanar da taron cikin yanayi na farin ciki, inda aka nuna ɗaliban da suka kammala saukar Alƙur’ani tare da bayyana irin ƙoƙarin da makarantar ke yi wajen bunƙasa ilimin addini da tarbiyyar yara da matasa.

By ukarofi

Leave a Reply