Malami Bukkuyum: Mutumin da ya shafe shekaru 35 yana facin hanyoyin Najeriya

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMAMAD a Nasarawa
 
Malami Bukkuyum, ɗan Jihar Zamfara ne, wanda ya shaida wa Manhaja cewa, ya kwashe shekaru 35 yana facin hanya bayan ya haƙo ƙasa ya cike ramummuka da ke manyan titina Najeriya.

Ba sabon labari ba ne mutum ya ce, ya bi titi a cikin biranen ƙasar nan da ya ke da ramummukan da sai direba ya zaɓi mai ƙarancin zurfi ya faɗa sannan ya wuce. Wannan ya sa matasa ko majiya ƙarfi suke gogoriyon saro ƙasa suna cike hanyoyi, domin neman na sa wa a bakin-salati a manyan da ƙananan hanyoyin ƙasar da ke cikin birane da kuma cikin ƙauyuka.

Abin mamaki shi ne, wannan bawan Allah da ya shahara, don yin irin wannan aiki, wanda daga jihar su ta Zamfara har ya zuwa Kudancin Nijeriya da garin Jebba da garin Alata da ke jihar Oyo, da dai sauransu. Amma a wannan lokaci ya yada zango ne a ƙauyen Dauda da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gurara a Jihar Neja, inda ya ke gudanar da wannan aiki.

Malami Bukkuyum Zamfara ya ce, ya shafe shekaru 35 yana wannan aiki, wanda a da shi kaɗai ya ke yi, amma dalilin samun abin duniya da ya ke yi, ya sa ya na da ɗan ƙaramin kamfani; kamfani mana, tunda yana da mutane kimanin biyar da ya ke jagoranta a wannan aiki na cike ramun da suke addabar matafiya a kan titinan ƙasar, a na ba shi hasafi.

Abin mamaki shi ne Malami ya ce, ba da rani kaɗai ya ke yin wanna aiki ba, domin idan ya yi shuka, sai ya dawo ya ci gaba da wannan aiki na sa-kai da kuma samun abin duniya na wani lokaci ya sami na taki, sannan ya koma gida ya amfana da kuɗin ya dawo ya nufi wata hanyar da ya ji labarin ba ta da kyau. Ya ce, a kan labari ya ke tsintar labarin hanyar da ta fi lalacewa, domin ya yi wa hanyar tsinke, saboda su riƙa cike hanyar ana kuma ba su nairori.

Malami Bukkuyum ya ce, wannan ne karon shi na farko a wannan hanya da ta yi matuƙar lalewa, wato hanyar Suleja zuwa Minna, wacce ta ke daura da babban birnin tarayya, Abuja.

A dangane da samun abin duniya kuwa, ya faɗi cewa, ta wannan aiki ya samu ya yi aure, inda ya na da mata da ’ya’ya bakwai. A dangane da ko nawa ya ke samu a wuni, ya ce, ya na kamawa daga Naira 2,000 zuwa Naira 4,000.

Amma ya ce, ya gode wa direbobi da fasinjoji da suke ba shi daga Naira 50 zuwa sama har a wani lokaci ana tsayawa a ba su takardar Naira mai darajar Naira 1,000. Amma wani hanzari ba gudu ba shine, halin ko-in-kula da manyan mutane masu wucewa a guje ana yi musu kuwwa na jiniya suke yi musu, waɗanda ya ce, su ne ba su yi gyaran hanyoyi ba kuma ba su taɓa ba su ko sisin-kobo ba balle su ce an gaishe ku.

Malami ya kuma gode wa Allah da masu tuƙi, don a wannan tsawon lokaci bai taɓa samun haɗari ba. Ya ƙara da cewa, suna yin dabarar saka jajeyen riguna, sannan suna dasa jajeyen tuta a gefen titina, don zama alama ga masu tahowa tun daga nesa, don su rage wuta, don ana gyaran hanya a gaba. Ya ce, wannan ya sa duk masu tafiya suke rage gudu idan sun tunkaro kusa da su.

Wannan bawan Allah ya ce, ganin yana samun abin duniya ya sa wasu a ƙauyensu suke bin sa, domin su ma su sami ƙaruwa. Wannan ya sa sauran ’yan kamfanin na kwangilar sa-kai suke rarrabuwa tsakaninsu inda shi Malami ya ke tsayawa shi kaɗai, sannan sauran suke yin aikin a gaba kaɗan da inda ya ke.

Ya ƙara da cewa, suna yin aikin ne daga safe zuwa yamma, sannan su je su huta sai kuma gobe, domin aiki ne ma gajiyarwa matuƙa.

Yayin da Manhaja ta tambaye shi ko ba ya son ganin an gyara titinan ƙasar, don ta nan ya ke samun abinci, sai ya ce, ya na matuƙar son ganin an gyara titina, amma ya ƙara da cewa, ko an gyara, ai sai an sami inda ya yi ramuka.

Bayanai dai sun nuna cewa, wannan lalacewar titina bai rasa nasaba da dalili yawan motocin ɗaukar kaya tunda titin jirgin ƙasa ba sa aiki, sannan ba a yin kwata ko magudanan ruwa a gefen titina, kuma hukumomi ba sa gyaran tituna tun ɓarnar na ƙarama kafin rami ya zama wagege.