Tasirin kwalliyar mata a gidan aure

Daga AMINA YUSUF ALI

Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon zan yi bayani a kan irin tasirin da kwalliyar ‘ya mace da gyaranta suke da shi wajen janyo mata daraja a gidan aurenta ko kuma akasin haka.

Da farko dai mu duba me ake nufi da kwalliya? 
Kwalliya dai tana nufin duk wani nau’i na gyara da mace za ta yi tun daga wanke can, gyaro can, shafa wannan, goge wancan da sauransu. Dukkansu suna cikin kwalliya ba sai ta fuska ba kaɗai.

Nau’ikan kwalliya:
Akwai irin su gyaran gashi a taje shi, ko a kitse shi ko a ɗaure da abin ɗaurewa mai kyau.

Sai kuma ƙunshi ja ko baƙi shi ma yana daga nau’in kwalliya da abubuwan da suke jan hankalin namiji. Sai kuma tsaftace farce/ƙumba a yanke shi a gyara. Masu hali sukan je wajen gyaran jiki (Salon) a gyara musu faratan. Wani ma har da gyaran ƙafa a wanke ta tas a goge kaushi.

Haka akwai gyaran jiki da akan yi a gurje jikin mace a cire gargasan kan fatarta dukka a gyara a sa fatarta ta dinga kyau da santsi da ƙyalli da ƙamshi. Irinsa ne gyaran jikin da ake wa amare.
 
Asalin kwalliya:
Kwalliya abu ce mai asali da tarihi ko a addinin musulunci. An rawaito a wani hadisi  lokacin da za a kai Nana Aisha gidan Annabi (SAW) sai da ‘yaruwarta Asma’u ta yi mata kwalliya da ado ta gyara ta. Sannan akwai wani hadisi da aka rawaito a kan mata suna zuwa wajen Nana Aisha neman yadda za su gyara kansu ga mijinsu. Sai Nana Aisha Allah ya ƙara mata yarda ta ce, da mace za ta iya ciro idanuwanta ta gyara shi saboda mijinta da ta yi.

Sannan kuma a tarihance, tun zamanin iyaye da kakanni akwai kwalliya. Su ma a wancan lokacin mata ba a bar su a baya ba. Suna yin ‘yan dabaru domin su ga sun yi kyau. Akan yi amfani da gawayi ko jar ƙasa ko tsirrai ko wasu abubuwan.
Mata sukan yi amfani da fure, a bakinsu ya yi ja kamar yadda muke sanya janbaki, haka idan an je kitso akan yi amfani da su manshanu da sauransu domin gashin ya yi kyau da taushi. Haka ana amfani da wani abu, shuni wanda ke sanya gashi baƙi sosai. Da wayewa ta fara zuwa kuma, sai aka fara amfani da su fankeke, hoda gazal, jagira da jambaki da sauransu.

Shin kwalliya tana da tasiri?
Wannan tambayar abun dubawa ce. Domin wasu matan sun kasance kwalliya ita ce rayuwarsu. Ba za su iya rayuwa ba ita ba. Kodayake mace da ma an san ta da yin kwalliya. Amma wasu matan ba ta dame su ba sam. Kuma suna da aure kuma da wahala a ce ba namijin da ba ya son kwalliya. Hasali ma yawanci ita kwalliyar ita ce farkon abinda yake jan hankalin namiji ga mace. Shi ya sa akwai wani azancin magana na Hausa da yake cewa, wai ‘ba a zaɓen mace ranar Sallah’.
 
Wato abinda azancin maganar yake so ya nuna shi ne, kowacce mace idan ta yi kwalliya tana da kyawun da za a dube ta kuma a ji ana son ta. Wato abinda ya sa wannan azancin ya yi wa maza garga]i shi ne, saboda kowacce mace mai tsafta da mara tsafta, mai kwalliya da mara kwalliya dukkansu suna yin kwalliya su yi kyau su fito ranar Sallah. Za ka iya yin kuskure ka zaɓo wacce ranar Sallar kawai ta yi kwalliya idan Sallar ta wuce ba za ta ci gaba da yi masa ba. Wannan yana ƙara nuna muhimmancin kwalliyar mace.

Mace ita ‘yar kwalliya ce ita. Kuma tana fara yi wa namiji kwalliya tun daga ranar da ya bayyana kansa a matsayin masoyinta. Koyaushe idan zai zo wajenta, takan yi ƙoƙarin gyara kanta ta yi masa kwalliya don faranta ransa. 
Haka za a cigaba har lokacin da za a yi auren. Ranar da za a kai masa ita ma, sai an caɓa mata ado don a sanya shi farinciki. Sannan idan tana amarci ma, za ta ci gaba. Amma daga tafiya ta yi tafiya sai a watsar a daina. Shi kuma namiji ɗan kwalliya ne kun ga sai zama ya ƙi daɗi ko kuma ya dinga hangen inda zai samo wacce za ta dinga yi masa kwalliya kamar yadda kike yi a da.

Kuma haƙiƙanin gaskiya kwalliya tana da tasiri tana kuma ƙara wa mace darajarta. Domin mace babu mummuna sai wacce ta ga dama. Idan kika ƙi yi kika zamar da kanki bera cikon bencin mata.

Haka mace idan tana kwalliya ko wajen ‘yanuwanki mata kin wuce wulaƙanci. Sai ki ga kin shiga ko’ina ana shayinki saboda kwarjinin da kwalliyar ta ba ki. Domin ita kwalliya na ƙara Mace ƙwarin gwiwa. Macen da ba ta kwalliya tana rasa karsashi kamar wacce take yi. Domin mace mai kwalliya da ado tana fita daban a cikin mata. Wacce ba ta yi sai rakuɓe-rakuɓe. 
Haka kwalliya makami ce ta riƙe miji. Su matan da yake hangowa a waje duk fa kwalliya ce. Wataƙila da za ki yi ke ma sai kin fi su fitowa. Ba macen da ta fi ki komai. Ke ma idan kika ga dama za ki iya gyarawa har ki wuce ta.
 
Kada kyau ko wani abu na mace ya tsorata ko ya razana ki. Ke ma kina da naki kyawun. Allah ba ya halittar banza. Dole ke ma kina da wani abun da ya birge shi ya aure ki. Sannan ko cikin kishiyoyi kike, ki dage da gyaran nan. Domin dole akwai dalilin da ya sa yake zaune da ke.

Akwai sirrin da mata ba su gane ba. Idan kun kai nawa gurin namiji, to dole akwai wani keɓantaccen abu da kike da shi wanda babu gare su. Don haka kada kowacce mace ta dinga yi miki kwarjini. Duk ɗaya kuke. Duk abinda ta yi ke ma za ki iya.

An san wasu mazan har da halinsu. Amma ke ma macen kina ba da gudunmowa wajen karkatar da hankalinsa zuwa ga  wasu matan. Ki dinga gyarawa. ‘yan ɗinkunan zamanin nan ki dinga yi. Ba lallai sai kin jawo abu mai tsada ba. Da kuɗinki kaɗan, dai-dai ruwa, dai-dai tsaki. Ki gyara. Amma gaskiya zaman nan a yi ta yawo da ɗaurin ƙirji ko kuma rigar bacci daga safiya zuwa yamma gaskia bai dace ba.
Kuma kwalliya ba sai da wasu kuɗaɗe da yawa ba. Wani lokacin ma sai ki yi kwalliyarki ki fito da ɗan ƙanƙanin kuɗi amma sai ki fi wadda ta kashe ku]i ta yi abinda ta yi don ta fito.
  
Sai ki ga, ga shi kin birge shi. Wani ma daɗin hakan zai sa ya yi miki alkhairi. Sannan ga ɗimbin ladan da za ki samu a wajen Allah. Sannan kuma ga shi kin ɗauke masa hankali daga wasu matan.

Sannan kuma rashin kwalliya yana sa tsufan mace ya fito. Sau nawa za ku ga mata ko maza ma shekaru sun ja, amma kwalliyar nan ta sa ta zama ta fi wasu yaran matan? Sai ka ɗauke ta sau ɗari ba ka ɗauke su ba. Kuma ke yarinyar idan kika yi wasarere da kanki za ki zamar da kanki da kanki tsohuwa tun da ƙuruciyarki.

Duk da dai wasu matan suna ƙorafi a kan mazan Hausawa ba a iya musu. Wai sai a yi kwalliya su ƙi yabawa. Wallahi suna yabawa a zuciyarsu. Kawai jin kai ne yake hana namiji nuna yabawa da ƙyasawarsa a kwalliyar matarsa.

Idan kina da shakku a kan haka kuma, ki ɗan yi fashi ki jera wasu ‘yan kwanaki ki gani. Za ki ga yadda zai kasa haƙuri sai ya tambayi me ya faru.

Kuma ke da kike yin kwalliyar ki ƙaddara kawai don kanki kike yi, kuma don Allah. Ki manta kina yi don ya ji daɗi. Haka kuma kar ki manta dukkan abinda kike yi, kina da lada a wajen Allah. Kuma kina ƙara danƙo a zaman aurenki.

Sannan akwai matan da suke ganin ba za su ɓata lokacinsu ba wajen yi wa mazan da ba sa gyara jikinsu kwalliya ba. Amma abinda ba ku sani ba, duk ƙazanta da rashin gyaran namiji yana son mace mai kwalliya da tsafta. Don haka ke ki gyara. Wani a sanadiyyarki shi ma zai koyi yin kwalliya da gyaran.

Haka shawara kyauta ga mata da mazajensu ke zaman majalisa da ƙin dawowa gida da daddare. Ku jiɓanci kwalliya koyaushe za ku sha mamakin yadda zai sauya ha dinga ɗokin dawowa kullum.

Don haka mata, don Allah mu gyara. Mu dage da kwalliya domin makami ce mai fasa zuciyar namiji ta dasa ƙaunarki a ciki.
 
A dage tun ana yi kamar ba a gani har ya zamana abin ya fara tasiri. Kada ki sake a bar ko a baya. Kada ki ƙasƙantar da kanki a kan hangen an fi ki. Ke ma ki yi amfani da naki makamin. Kuma mace ta sani, garin kwalliya kada ki ce za ki wuce gona da iri wajen canza kanki. Misali launin fatarki. A’a ki zauna yadda Allah ya yi ki.

Abinda Allah ya ba ki, ki yi haƙuri da shi ki inganta shi. Sai ki ga kin haska. Allah ya iya mana. Bissalam.

Mu haɗu a mako na gaba.