Manchester City ta rage tazarar tsakaninta da Arsenal zuwa maki uku bayan doke ta da ci 2 da 1

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gasar Premier League na ƙasar Ingila ya sake ɗaukar wani salo bayan da ƙungiyar Manchester City ta doke Arsenal da ke kan teburin gasar da ci 2 da 1 filin wasa na Etihad.

Wannan sakamako ya rage tazarar da Arsenal ta ba City a teburin gasar zuwa maki uku yayin da ita kuma Cityn take da wasa ɗaya a hannu.

Ɗan wasa Rayan Cherki ne ya fara zura ƙwallo a ragar Arsenal a minti na 16, inda bayan mintina biyu murnar magoya bayan City ta koma ciki a lokacin da Kai Havertz ya farke bayan kuren mai tsaron gidan City, Gianluigi Donnarumma.

Bayan koma wa hutun rabin lokaci ne ɗan wasan gaba na City da Norway, Erling Haaland a minti na 65 ya zura ƙwallo ta biyu, wanda ya ba wa mai masauƙin baƙi damar yin nasara a wasan.

A yanzu dai City za ta yi wasa guda a tsakiyar mako, inda za ta kara da Burnley a filin wasa na Turf Moor. Da zarar ta yi nasara, za ta haye kan teburin Premier League da yawan ƙwallaye.

By Babaji