“Me ya sa mutane ba sa taya mu yarda da ƙaddara kan cutar da muke tare da ita”
Daga AISHA ASAS
Cutar amosanin jini, wato sikila cuta ce da ke da matuƙar wuyar sha’ani, wani lokacin akan yi wa masu ita kallon masu ƙarancin rayuwa kasantuwar ba sosai ne suke wuce lokutan ƙurciya ba.
Cutar sikila cuta ce ta gado, ma’ana akan same ta ne ta sanadiyyar kalar jinin da iyaye suke da shi. Wannan na nufin takan samu ne idan iyayen biyu suna ɗauke da sinadarin cutar kamar AS ya haɗu da AS, ko kuma wani ɓangare AS da SS.
Sikila cuta ce wadda za mu iya kira mafi takurawa da tsananin zafi mai jimawa tare da ƙarancin lafiya a kodayaushe, ta kan taka muhimmiyar rawa wurin hana mai ita cikar burinshi ta fuskar karatu ko burin zama wani abu da ya jima yana son kai wa, ba don komai ba kuwa face yawan ciwo da ya fi kwanakin lafiya yawa a rayuwarsu.
Duk da cewa cutar ba ta zaɓar jinsi kasantuwar tana samuwa ne ta hanyar gado daga iyayen da suka haife ka, saidai sau da yawa ƙalubalen cutar kan yawaita ga mata, wataƙila ko don su ne masu kula da gida, kuma aurensu ake yi ba su ke aure ba.
Sau da yawa maza masu ɗauke da wannan lalurar sukan samu wasu ababe da yawa fiye da mata masu ɗauke da ciwon, misali, aure; a yanzu ne ma da ake wayar da kai sosai kuma mutane suka fara ankara da cutar sosai, har ake samun wasu iyaye na tsayin daka wurin ganin anyi bincike kafin su haɗa auren, amma duk da haka da yawan maza sukan samu matan aure ba tare da wani ƙalubale ba. Wanda a ɓangaren mata ba haka ba ne.
Da wannan ne shafin Gimbiya na wannan mako ya gayyato ɗaya daga cikin bayin Allah da ke ɗauke da wannan lalurar don jin irin yadda take fama da kuma yadda cutar ta kawo tsaiko a rayuwarta a matsayinta ta mace. Idan kun shirya Aisha Asas ce tare da Khadija Muhammad Baba.
MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki ga masu karatu, ciki har da abin da ki ke yi a rayuwa?
KHADIJA BABA: Assalamu alaikum. Sunana Khadija muhammad Baba, ni maɗinkiya ce, ina kuma taɓa ƙananan kasuwanci na cikin gida irin namu na mata.
Yaushe aka gano kina da lalurar Sikila, kuma yaya hakan ya shafi rayuwarki tun daga wancan lokaci?
An gano ina da lalurar Sikila ne tun ina wata shida a duniyya, ma’ana dai tun ban san kaina ba. Tun a lokacin iyayena suka shiga ɗawainiyya da ni. A cewarsu ba su ma zace zan rayu ba, kan irin halin da nake shiga. Sun sha wahala kaina matuƙa. Kuma ni kaɗai ce suka haifa mai ɗauke da irin lalurar.
Yaya rayuwarki ta yau da kullum take kasancewa da wannan lalura?
Rayuwata ta yau da kullum ta kasance ba mai daɗi ba, takai har karatuna sai da ta taɓa. Na taso a yarinya mai son karatu, amma da na je makaranta yau, gobe sai kuma na kwanta ciwo. Sanadin haka aka hanani zuwa makaranta a wancan lokacin, ganin irin wahalan da nake sha. Kuma ƙarin abin iyayena ba masu ƙarfi ba ne, duk da hakan sun yi ƙoƙari da ni matuƙa. Yanzu haka dai ma na rasa su dukka biyun. Allah Ya sa Aljanna ce makomarsu.
Waɗanne manyan ƙalubale ne ki ka fuskanta a rayuwa sakamakon lalurar Sikila?
Gaskiya akwai ƙalubale sosai musanman akan aure da da ina ganin ƙalubalen mai sauƙi ne, saidai ina har yanzu ban tsallake wannan ƙalubalen ba. Kuma na tabbatar duk wata mai irin lalura ta ta taɓa cin karo da irinsa koda sau ɗaya ne a rayuwarta. ƙalubalen kuwa shi ne, samun mijin da zai aminta da aurenki a halin da ki ke ciki. Da zaran an zo neman ki aure, ki ka sanar da shi gaskiya kan halin da ki ke ciki, sai ya ce ba zai iya ba. Wasu ma fakewa suke yi da lalurar ta masu kuɗi ce. Ko kuma wasu iyayensu ne za su hana su auren wai kar kuɗinsu ya ƙare wurin nema maki lafiya.
Wannan abu na taɓa mini rayuwa matuƙa, kuma ina ƙara gode wa iyayena, domin su ba masu hali ba ne, amma haka suka yi ƙoƙari kaina, har Allah Ya raya ni, na girma. Babu taimakon kowa sai na Allah. To me ya sa mutane ba sa taya mu yarda da ƙaddara. Me ya sa ba sa ƙarfafa mana gwiwa na mu yarda da ƙaddara. Maimakon haka sai suke nisanta kansu da mu.
Wane irin kulawa ki ke samu daga ɓangaren likitoci da iyalanki?
Alhammdulillah likitoci suna ƙoƙari dazaran an kai marar lafiya kuma aka ce wannan sikila ce, to za kaga sun yi abinda ya dace cikin gaggawa. Domin ina ganin tausayi a idonsu lokuta da dama. ɓangaren iyalaina kuwa ba abinda zance face Allah kaɗai ne zai saka masu da alheri. Domin ba ni da bakin gode masu, sai fatan Allah ya sa sanadin shigarsu Aljanna ce. Bakina ba zai bar yi masu addu’ar rahma ba har ƙarshen numfashina.
A cikin al’ummarmu, ana ba batun aure muhimmanci sosai. Yaya ki ka kalli wannan ɓangare a rayuwarki?
Al’ummarmu har yanzu fa sun kasa fahimtar ita kanta cutar ta sikila. Ita fa ba ɗaukarta ake yi ba, amma yadda ake tsoronta ko mai cutar ƙanjamau albarka. Ga manyan curuta nan kamar ciwon hanta, ƙoda da sauransu, amma duk an fi tsoron cuwon sikila sama da su. Kuma sun kasa gane ba fa kowane haɗi ne za ka iya haihuwar sikila ba. Koda kuna da yiwar haihuwar mai ita, ba lallai ba ne ku haife su ɗin.
Shin lalurar sikila ta taɓa yin tasiri a kan damar samun abokin rayuwa?
Sosai kuwa. Ga shi ina da shekaru 44 ba ni da aure, saboda ana gudu na, dalilin ina sikila.
Kin taɓa fuskantar ƙalubale ko matsin lamba daga iyali ko al’umma dangane da batun aure?
Sosai ma. Saboda ana ganin na ƙi yi ne da ganga saboda suna ganin ana zuwa wurina. Abinda ba su sani ba, da zaran ka faɗa wa mutum halin da ka ke ciki, sai ya ɗauke ƙafa. Wasu kuma sukan faɗa maka ba za su iya ba kafin su ɗauke ƙafa. To da yake ba zama za ka yi kana sanar da mutane yadda lamarin ke gudana ba sai su yi ta ganin kai ɗin ne ba ka san yin auren, nake koran su. Wasu kuma dama ba auren ne ke kawo su ba, ire-irensu da na fuskanci hakan sai na sallame su.
Yaya ki ke sarrafa irin waɗannan matsin lamba ko tambayoyi daga jama’a?
Ba ta yadda nake sarrafa lamarin face ta hanyar tawakali. Na riga na yarda da ƙaddarata. Abinda nake sanar da kaina a kullum shi ne, aure, haihuwa da kuma mutuwa duk daga Allah ne, suna hannun Allah kuma lokaci ne, sai lokacin ya yi ne za a yi.
Waɗanne abubuwa ne ke baki ƙarfin gwiwa da kwarin gwiwa a rayuwa duk da wannan yanayi?
Na rungumi haƙuri da kuma bar wa Allah ikonsa da na riƙe su ke sa a kodayaushe ina cikin farin ciki.
Akwai wasu nasarori ko abubuwan da kika cimma da ki ke alfahari da su?
ƙwarai kuwa. Akwai tsawon rai, na yi tsawon rai, domin masu wannan lalurar da suka kai shekaruna ba su da yawa. Hakan kuwa babbar nasara ce domin duk abinda ka ke ciki ibada ce ka ke yi.
Wane irin fahimta ki ke so al’umma su yi game da masu lalurar sikila, musamman mata?
Ina so al’umma su fahimci cewa, Allah ne ya ƙaddara yin mu a hakan tun muna cikin cikin mahaifanmu. Don haka muna buƙatar tausayawa da taimako. Kuma su taya mu yarda da ƙaddararmu.
Kin taɓa fuskantar wariya ko rashin fahimta daga jama’a saboda yanayinki?
Babu wariya sai tausayawa sosai.
Me ki ke yi don rage wannan ciwo na sikila mai tsanani da kula da lafiyarki?
Ba na sa damuwa a raina. Kuma ina yawan neman shawarwari daga wurin likita. Sannan ina shan maganina yadda yakamata.
Wane saƙo ki ke da shi ga sauran mata masu lalurar sikila?
Su cire duk wata damuwa a ransu, su san cewa, a kullum cikin ibada suke. Su sa a ransu wannan ita ce ƙaddararmu, tare da yin fatan Allah ya bamu ikon cinyewa.
Me za ki ce ga iyaye da matasa dangane da muhimmancin gwajin sikila kafin aure?
Alhammdulillah a yanzu kai ya waye, ana yin gwajin kafin aure daga birni ko har karkara. Duk da haka akwai masu taurin kai da suke da ƙiyawa. Ina kira da su yiwa ‘ya’yansu wannan gatan tun kan su haifo su.
A ganinki, wane irin tallafi ya kamata gwamnati ko ƙungiyoyi su ƙara bayarwa ga masu lalurar sikila?
Talafin magani ko jini. Akwai masu lalurar da ke buƙatar jini idan lalurar ta taso masu, saidai rashin samun tallafi daga gwamnati kansa su shiga mawuyacin hali. Duk da cewa, wasu jihohin suna samu. Amma dai wannan ne buƙatar mu har wajen ƙungiyoyin da abin ya shafa.
Duk da rashin aure zuwa wannan lokaci, yaya ki ke kallon rayuwarki da makomarki gaba ɗaya?
Narigada na daima damun kaina akan batun aure, na karkata hankalina wurin ganin na samu makoma mai kyau.
Me ke baki farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwarki?
Na ganni a cikin ‘ya’yan ‘yan uwana, domin sun mayar da ni tamkar ƙawarsu. Muna wasa da dariya. Sosai ina jin daɗin hakan.
Idan za ki bai wa al’umma shawara guda ɗaya kan yadda za su riƙa mu’amala da masu irin wannan lalura, me za ki ce?
Su dinga tausaya wa masu lalurar sikila, masu ƙwayar halitta AA su dinga aurenmu. Ko mazan ko matanmu, domin da muna da damar auren junanmu kamar masu cutar ƙanjamau da wallahi an sha mamaki, saboda muna da tausayin juna sosai. Muna da wani sirri na zamantakewa, ga shi ba mu da hayaniya, domin a kullum tunanin mutuwa ne a ranmu. Da zaran mun fara ciwo, to fa za mu fara tunanin lokaci ya yi. Haka muke a kodayaushe. Daga ƙarshe ina roƙon gwamnati da ta taimaka mana, domin yawancin iyayenmu ba masu ƙarfi ba ne sosai.
