Malaman makaranta a Abuja sun fara yajin aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Malaman makarantun sakandare da framare na gwamnati a Birnin Tarayya Abuja sun shirya fara zanga-zanga a yau Litinin, bayan wani umarni daga majalisar zartarwar (SWEC) Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa.

An fitar da umarnin ne bayan wani zaman gaggawa da aka gudanar a Gwagwalada, Abuja a ranar Juma’a. Shugaban reshen birnin, Abdullahi Shafa; Sakatariya, Margaret Jethro; da Sakataren yaɗa labarai, Ibukun Adekeye ne suka fitar da sanarwar.

A ciki, ƙungiyar ta umarci dukkan malamai da su janye daga gudanar da ayyukansu da jiran umarni na gaba akan al’amarin.

Haka kuma, an shawarci iyaye da su zaunar da ‘ya’yansu a gida har sai an sake fitar da wani saƙo, tana mai cewa za a cigaba da yajin aikin har sai an biya dukkan buƙatun da suka gabatar.

Wannan na zuwa ne bayan wa’adin mako guda da ƙungiyar ta ba Ministan Abuja Nyesom Wike a ranar 11 ga Maris ya ƙare. Ƙungiyar ta kuma sake ƙara wasu kwanaki 28 ga hukumomi, waɗanda suka ƙare ba tare da an ɗauki mataki akan buƙatun nasu ba.

Duk da cewa gwamnatin ta fara aiwatar da biya da sabon tsarin biyan albashi na N70,000 da biyan bashin wata tara ga malaman framare, ƙungiyar ta ce har yanzu akwai buƙatu da dama da ba a warware ba.

By Babaji