Manoma a Katsina sun koka yadda wata tsutsa ke addabar gonaki

Spread the love

Manoman hatsi dake Katsina sun koka kan yadda wata tsutsa ke addabar gonakin su. A wani ziyara da kamfanin jaridar News point yayi a babban birnin jihar Katsina, ya samu labarin lamarin ƙara ta’azzara yake a gonaki cikin yan kwanakin nan.

Wasu manoma da abin ya shafa, sun ce suna tunanin abin na ƙara yawa ne saboda rashin ruwan sama, gashi manoma da dama sun kammala yin shuka.

Yanzu dai manoman sun dauki matakin amfani da maganin ƙwari domin magance tsutsar. Da suka zagaya, haka abin yake a ƙauyuka da dama irin su, Autawa, Bambami, Daba, Sabon Gida, Dabaibayawa, Angawa, da Makaɗa a cikin ƙaramar hukumar Ɓatagarawa.

By ukarofi