Kuɗin da aka ware don gyara gidan sarki na Nasarawa a Kano ya jawo kace-nace

Spread the love

A yayin da ake ta kai da kawo a kan masarautar kano, gwamnatin kano ta ware miliyan N99.9 domin gyaran gidan sarki na Nasarawa wanda tsohon sarki Aminu Ado ke ciki.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Aminu Dantiye ya bada sanarwar a taron manema labarai. Dantiyen yace, kuɗin da aka ware, za ai amfani dasu wajen gyaran katanga da kuma harabar gidan sarkin.

Ya cigaba da zayyano wasu aikace aikace da gwamantin ta sahale za ayi. Amma ba wanda ya ɗau hankali kamar kuɗin da aka ware domin gyaran gidan sarki.

Wata ƙungiya mai zaman kanta mai sunan ” war against injustice” ta fito tayi Allah wadai da wannan almubazzaranci da gwamnatin ke shirin yi.

By ukarofi