Marasa lafiya daga jamhuriyyar Nijar na shigo wa Nijeriya neman magani

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Duk da tsamin dangantaka da ke akwai tsakanin Nijeriya da Nijar akwai yan ƙasar Nijar da ke shigowa Nijeriya neman magani .

Rabi Sani daga ƙauyen Daga a garin Maraɗi ta ce ta zo garin Magama a ƙaramar hukumar jibiya domin a duba lafiyar yaron a babban cibiyar shan maganin na Magaman Jibiya.

Tace yaron ta na fama da gudawa ne kuma ya sami kula da ya kamata.

Ta fadawa manema labarai cewa mutanen su daga Nijar na shigo wa a kullum domin neman magani.

Haka wasu marasa lafiya daga Nijar da suka zo neman magani a asibitin sun shaida wa manema labarai cewa tunda suke zuwa asibitin jibiya ba a taɓa tsangwamar su ba.

Ɗahiru Magaji shine mai kula da babban cibiyar shan magani na Magama ya shaidawa manema labarai cewa lalle marasa lafiya daga Nijar na neman magani, har mata da ƙananan yara masu fama da ciwon cimaka.

Ya ƙara da cewa yawancin marasa lafiya daga garuruwan Ɗan Isa,Faru,kare da Hirji ke zuwa kullum shan magani.

By ukarofi