Masarautar Koko ta yaba wa Gwamna Nasir kan ƙirƙiro hakimai takwas

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Masarautar Uban ƙasar Koko da ke jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mohammed Bello Koko II ta yaba wa Gwamna Malam Nasir Idris bisa ga ƙirƙiro sababbin hakimai guda takwas daga cikin masarautar.

Ya yi wannan bayanin ne a fadar sa da ke garin Koko sa’ilin da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja ranar Larabar da ta gabata.
Basaraken ya ce, A madadin sa da ilahirin al’ummar wannan masarautar ta Koko suna miƙa godiya ga mai girma gwamna Malam Nasir Idris da kuma masarautar Gwandu bisa ga wannan gagarumin mataki na ƙara yawan hakimai a ƙarƙashin masarautar Koko, ta hanyar ƙirƙirar sababbin muƙaman hakimai guda takwas (8).

Wannan mataki na mai girma Gwamna ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar Koko suka daɗe suna fatan samun ƙarin hakimai domin ƙarfafa tsarin shugabancin gargajiya, sauƙaƙa gudanar da al’amuran jama’a da kuma ƙara samar da cigaba a gundumar Koko.
Saboda haka, wannan amincewa da Mai Girma Gwamna ya yi ba ƙaramin abin farin ciki ba ne ga al’ummar masarautar Koko.
Muna kallon wannan mataki a matsayin amsa ga wata muhimmiyar buƙata da jama’ar Koko suka daɗe suna nema, tare da nuna cewa gwamnatin Mai girma Gwamna tana sauraron muradun jama’a tare da ɗaukar matakan da suka dace domin inganta rayuwar su.

Ya bayyana cewa babbar hikima a cikin ƙirƙiro waɗannan sababbin hakimai shi ne yin kowacce inda ta dace da kuma zaƙulo waɗanda suka dace saboda ƙirƙirar waɗannan mukamai zai taimaka matuƙa wajen ƙara kusantar shugabancin gargajiya da al’umma, inganta sadarwa tsakanin jama’a da hukumomi, da kuma samar da ingantacciyar hanyar magance matsalolin al’umma cikin hikima da lumana.

Daga ƙarshe basaraken ya taya sababbin hakiman da aka naɗa murna, tare da addu’ar Allah ya ba su hikima, basira, da ikon yin adalci, gaskiya da amana tsakanin al’ummar da ke ƙarƙashin su.

Sarakunan da aka naɗa dai sun haɗa da Kabiru Sama’ila Danduste a matsayin Hakimin Dandashe,
Alhaji Salihu Bello Hakimin Unguwar Albarkawa, Sama’ila Abdullahi Tukura Hakimin Unguwar Gwadabawa, Abdullahi Salihu Hakimin Unguwar Wurya, Mustapha Muhammad Hakimin Unguwar Illo, Alhaji Ahmed Salihu Hakimin Unguwar Mallamawa, Alhaji Musa Salihu Hakimin Kawo sai kuma Alhaji Ibrahim Salihu Koko (Sarkin Kudun Koko) a matsayin Hakimin Unguwar Rafin Kada.

By ukarofi

Leave a Reply