Masari ya yi tir da yadda jami’an tsaro ke kashe mutane da tuƙin ganganci a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi tir da yadda ake samun aukuwar yadda jami’an Hukumar Kwastam ke kashe ‘yan jihar saboda tuƙin ganganci da abubuwan hawa.

Gwamnan ya bayyana ɓacin ransa ne cikin wata sanarwa wadda Darakta Janar na Yaɗa Labaran Gwamnatin Jihar, Abdu Labaran Malumfashi, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.

Masari ya ce, daga wannan lokaci gwamnatinsa ba za sake lamuntar aukuwar irin haka a jihar ba.

Gwamnan ya yi magana ne a matsayin martani dangane da mummunan haɗarin da ya auku a Litinin da ta gabata a jihar, inda wani jami’in Kwastam ya murƙushe mutum takwas har lahira da motar aiki, a yankin ƙararmar hukumar Jibia.

Masari ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa ta’aziyyarsa ga ‘yan’uwan waɗanda suka rasu a haɗarin, tare da jajanta wa ‘yan’uwan waɗanda suka jikkata.

Ya ce daga yanzu gwamnatin jihar ba za ta naɗe hannu ta zuba ido tana kallon ana kashe ‘yan jihar masu biyayya ga dokoki ba saboda tuƙin ganganci daga jami’an gwamnatin da su ya kamata su kare rayukan jama’a.

Ya ce gwamnati na shirin ɗaukar mataki na shari’a a kan Hukumar Kwastam don ya zama izina ga sauran jama’a da kuma hana aukuwar hakan a gaba.