Za a yi wa Lai Mohammed wankan sarauta a matsayin Kakakin Kebbi a Satumba

Ranar 25 ga Satumba mai zuwa Sarkin Argungu a jihar Kebbi, Alhaji Mohammed Mera, zai naɗa Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a matsayin Kakakin Kebbi.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya samu a ranar Juma’a.

A bara ne Sarkin Argungu ya sanar da naɗa Lai a muƙamin yayin da yake bayyana tsare-tsaren bikin kamun kifi a Abuja da aka saba gudanarwa a Argugun wanda aka gudanar daga 11 zuwa 14 ga Maris na 2020.

Sanarwar ta ce an yi nisa da shirye-shiryen wankan sarautar da za a yi wa Ministan. Tare da cewa, Masarautar Argungu ta yanke shawarar yi wa Lai rawani a masarautar ne saboda ƙoƙarin da yake da shi wajen rayawa da kuma ɗaukaka al’adun al’ummar Nijeriya a idon duniya.

Haka nan, ta ce ƙoƙarin Ministan ya yi dalilin samar da ayyuka da kuɗaɗen shiga tare da wayar da kan matasa ta hanyar shirya bukukuwa da kuma baje kolin al’adu.

Kazalika, sanarwa ta nuna Masarautar Argungu ta yi la’akari da irin biyayya da kuma aiki babu son zuciya na Minista Lai, wanda a sakamakon hakan Nijeriya ta ƙara samun mutunci a idon duniya.

Masarautar ta ce, ƙwazon Ministan ya haifar wa bikin kamun kifi na Argungu samun tagomashi wanda har ya kai ga bikin ya samu shiga kundin UNESCO a 2016.

Sanarwar ta ƙara da cewa, wankan sarautan na daga cikin jerin abubuwan da aka shirya aiwatarwa yayin bikin Ranar Yawon Shaƙatawa ta Duniya da zai gudana ranar 27 ga Satumba, wanda Jihar Kebbi ce mai saukar baƙi.