Dattijon ƙasa, Ahmad Joda, ya kwanta dama

Daga AMINA YUSUF ALI

Allah ya yi wa ɗaya daga cikin fitattun manyan Ƙasar Nijeriya, Ahmad Joda rasuwa. Ya rasu yau Juma’a, a garin Yolan Jahar Adamawa. Marigayin ya rasu ne bayan matsananciyar doguwar rashin lafiya wacce ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Marigayin ya rasu ne yana da shekaru 91 da haihuwa. Kuma tsohon ɗan jarida ne wanda ya yi shuhra a fagen. Haka nan, yana ɗaya daga cikin manyan Sakatarorin Gwamnatin Ƙasar nan a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon, yayin mulkin soja. A inda ya yi ritaya a matsayin babban sakataren ma’aikatar masana’antu.

Bayan Yaƙiin Basasa ne a shekarar 1967, aka ba shi muƙamin babban sakataren inda ya riƙe wannan muƙamin daga 1962 zuwa 1967. Ya yi aiki tare da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da ta Ilimi da kuma ta masana’antu. Ya yi ritaya a shekarar 1978.

Marigayin ya taɓa zama ɗan majalisa a 1988. An naɗa shi Shugaban Kwamitin Yaƙi da fatara a 1999 domin ya dinga ba wa Shugaban Ƙasa shawara a kan harkar.

Bugu da ƙari, ya riƙe muƙamin shugaba ko shugaban masu ruwa da tsaki a ɓangarori da dama na gwamnatin ƙasar nan. Misali, ya sha zama Shugaban Kamfanin Albarkatun Man Fetur (NNPC), da sauransu.

An haifi Joda ne a garin Yola na Jahar Adamawa a 1930 inda ya yi karatunsa na firamare da sakandare a Adamawa kafin daga bisani ya shiga Barewa College a 1945. Ya rasu ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.