Yadda kyakkyawar zamantakewa ke kawo zaman lafiya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A wannan mako ina son hankalin mu ya karkata ne wajen nazarin yadda halayya ta gari da kyautatawa juna a mu’amala ta yau da kullum ke iya haifar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama’a, musammam mutane masu bambancin ƙabila, addini ko ra’ayin siyasa, da sauran harkoki da zaman tare ke iya haɗa jama’a, daga ɓangarori daban-daban.

Babu shakka zaman lafiya da jama’a, tausayawa, tallafawa, da kauce wa duk wani abu da zai iya kawo saɓani da rashin fahimta a tsakanin mutane, abin a yaba ne matuƙa, babu ma kamar wannan lokaci da jama’a ke cikin ƙunci da rashin yarda da juna, saboda kurakuran da suke zargin wasu suna yi da gangan, don cimma wata manufa ta son ran su, ko danne haƙƙin wasu.

Rashin yarda, zargin juna, hassada, kishi, zalunci, babakere, da tauye haƙƙin raunana, halaye ne da aka saba gani a zamantakewa ta yau da kullum, inda wasu ke ƙoƙarin fifita kansu da tilasta buƙatun su kan na sauran mutane, a dalilin haka kuma sai a samu turjiya da nuna rashin yarda daga wani ɓangare.

Mummunar halayya irin ta hassada na ruguza imani da mutuncin mutum, saboda kasancewarta mugun ciwon da ke nuƙurƙusar mai yin ta a cikin zuciyarsa shi kaɗai.

A taƙaice, idan aka ce HASSADA ana nufin wani yanayi da mutum zai riƙa jin wani zafi, rashin kwanciyar hankali, ko ɓacin rai a yayin da ya ga wani ɗan uwansa, maƙwabci, aboki ko ma dai wani na kusa da shi da Allah ya yi wa ɗaukaka, ko wani alheri da shi bai samu ba.

Wasu manazarta sun kasa hassada zuwa gida uku, inda suka nuna cewar, akwai hassada ta jin ƙyashi, yayin da mutum ya ji a zuciyarsa don me wani zai fi shi samun wani abu a rayuwa. Kamar misalin kuɗi, mulki, baiwa ko muƙami.

Haka kuma mutum ya kan ji shi ba ya son kowa ya samu wani abin alheri ko ƙaruwa sai shi kaɗai. Sai na uku wanda shi ne ya fi kowanne muni, wato mutum ya ji cewa idan dai shi ba zai samu abu ba to, gara kar kowa ma ya samu. Irin su ne suke zama ‘yan a fasa kowa ya rasa.

Mutane da yawa suna faɗawa cikin aikata hassada ba tare da sun ankara ba. Alal misali, Yawan yin magana a kan ci gaban wani ko wata. Har ya kai ga cewa, ‘aw! su wane an haye, sai ka ce da ba teburin mu daya ba a wajen aiki, lokacin nan kuwa kayansa ba su wuce kala biyar ba.’

Haka nan kuma mutum ya kan riƙa ambaton cewa, ‘Su wane an samu shiga, ji wai yanzu shi ne kaza, sai ka ce ba tare muke cin kwakwa ba.’

‘Dubi daga malami ya shigo aji sai ya fara wani iya yi wai shi a dole mai ƙwaƙwalwa.’

Yadda mutum zai gane idan ya fara nuna halayyar hassada shi ne, yawan nuna damuwa da al’amarin wani ko wata, wanda kwata kwata bai shafe ka ba. Damuwa da son sanin halin da wata ko wani yake ciki. Idan ka ji mummunan labari game da wani ka ji daɗi a ranka, ko ma ka yi dariya ko shewa, idan kuma ka ji labari mai daɗi game da mutum sai ka ji ranka ya ɓaci, ka kasa yi masa fatan alheri, ka fara jin tsoron kar ya wuce ka a wani mataki na rayuwa. Sai ka fara qoqarin kai sukarsa a wajen abokan arzikin sa, ko ƙoƙarin faɗin miyagun maganganu game da shi, ko kuma faɗin kalamai na ɓatanci game da shi, musamman ma idan ba a tambayeka labarinsa ba.

Hassada tana hana mai yinta samun cigaba a cikin rayuwarsa da kuma duk abin da ya sa gaba ba zai ga nasara bayyananniya a kai ba. Hassada tana rage imani kuma tana taimakawa wajen aikata shirka da fita ma daga addini ba tare da mai yin hassadar ya sani ba.

Ya kamata mutum ya yi ƙoƙarin ganin ya yaƙi wannan mummunar halayya ko kare kansa daga gare ta. Kuma gane yadda zai iya cimma haka ba wani abu ne mai wuya ba, saboda ai yin hassadar ta fi wuya! Takurawa kan mu muke yi, sai mun yi hassadar duk kuwa da mun san illarta da kuma nauyin zunubinta.

Na farko, mutum ya yi ƙoƙarin cire kansa a kan duk wasu al’amuran da ba su shafe shi ba. Kuma ya yi ƙoƙarin ya mayar da hankalinsa a kan inganta rayuwarsa. Sannan ya kiyaye kansa daga ƙananan gulmace-gulmace. Son iyawa ko son ba da shawara a inda ba a nemi taimakonsa ba. Mutum ya kuma kasance