Masu shigo da man fetur za su yi wa matatar Ɗangote zagon ƙasa – Obasanjo

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Toshon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana shakku kan samun nasarar matatar man fetur ta Ɗangote wadda ta fara aiki a kwanakin baya.

Matatar man fetur ta Dangote wadda hamshaƙin ɗan kasuwar na Afirka ya narkar da kuɗi dala biyan 20 wajen samarwa, ana sa ran za ta iya tace ganga 650,000 na ɗanyen mai a kowace rana.

Sai dai a baya-bayan nan an samu taƙaddama tsakanin Dangote da gwamnatin Nijeriya, bayan da ɗan kasuwar ya yi zargin cewa ana yi masa zagon ƙasa.

A tattaunawar da Obasanjo ya yi da jaridar Financial Times, ya ce “Idan masu sayarwa ko samar da tataccen man fetur suka ji tsoron za su rasa maƙudan kuɗin da suke samu, za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun karya masa gwiwa.”

A cikin watan Disamban 2023 ne matatar man fetur ta Dangote ta karɓi ɗanyen mai ganga miliyan shida.

Sai dai daga baya matatar ta riƙa shan wahala wajen samun ɗanyen man fetur domin ci gaba da ayyukanta.

Aliko Dangote ya zargi kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL da gaza samar masa da isasshen man fetur da yake buƙata.

Sannan ya ce hannun jarin da NNPLC ɗin ke da shi a matatar ya koma kashi 7.2 cikin ɗari a madadin kashi 20 cikin ɗari da aka tsara a baya.

A cikin tattaunawa Dangote ya ce: “Dama mun yi tsammanin za su mayar da martani ta hanyar ƙin samar da ɗanyen man fetur da ƙin sayen tataccen man fetur ɗin. Amma wannan na wani ɗan lokaci ne, za mu yi nasara.”

By ukarofi