Mata 2,900 kowace za ta samu tallafin N20,000 a Binuwai

Daga AISHA ASAS

Ministar Jinƙai, Agaji da Kyautata Rayuwar ‘Yan Kasa, Sadiya Umar Farouq, ta jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta neman fitar da talakawa da marasa galihun ƙasar nan daga ƙangin talauci.

Ministar ta ce kimanin mata 2,900 ne gwamnati ta tallafa wa da kuɗi N20,000 ga kowannensu a jihar Binuwai ƙarkashin shirin musamman na Gwamnatin Tarayya na tallafa wa matan karkara a Binuwai da kuɗi don kama sana’a.

Sadiya ta yi waɗannan bayanai ne a wajen bikin ƙaddamar da rabon tallafin ga matan karkara a Binuwai, in ji sanarwa da ta fito ta hannun Mataimakin Daraktan Labarai na ma’aikatar Ministar, Rhoda Ishaku Iliya.

A cewar Sadiya, an samar da shirin tallafa wa matan karkarar ne a 2020 saboda manufar da gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke da ita na kyautata rayuwar ‘yan ƙasa.

Ta ce, “Shiri ne da gwamnati ke son yin amfani da shi wajen tsame ‘yan Nijeriya milyan 100 daga ƙangin talauci a tsakanin shekaru 10. An tsara shirin ne ta yadda za a tallafa wa matan karkara da ke fama da talauci da marasa galihu da kuɗi a duk faɗin ƙasa.

“A ƙarƙashin shirin ana sa ran a raba wa mata 125,000 a faɗin ƙasa kuɗi N20,000 ga kowacce a tsakanin jihohi 36 da ake da su har da birnin tarayya, Abuja. Ƙudurinmu a jihar Binuwai, shi ne mu tallafa wa mata 2,900 a tsakanin duka ƙananan hukumomi da jihar ke da su”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *