Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Alƙaluman da Hukumar Zaɓen Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta fitar kan rajistar masu zaɓe da hukumar ke gudanarwa sun nuna cewa mata da matasa ne kan gaba a yawan masu rajista ta intanet da kuma masu zuwa cibiyoyin da hukumar ta keɓe don yin rajistar.
Hukumar ta ce, ya zuwa ranar Lahadi 7 ga watan Satumba mutum miliyan 3,544,850 ne suka yi rajistar ta intanet, mako uku bayan fara shi ranar 18 ga watan Agusta.
Bayanan rajistar da hukumar ke wallafa wa a shafinta na ɗ, sun nuna cewa jihar Osun ce kan gaba a yawan masu rajistar, inda take da mutum 518,635.
Sannan jihar Legas ke biye da masu rajista 440,647, sai jihar Ogun mai mutum 348,217.
Alƙaluman da INEC ɗin ta fitar sun nuna cewa yankin kudu maso gabashin ƙasar ne koma-baya wajen rajistar masu zaɓen.
Jihar Ebonyi ce mafi ƙarancin masu rajistar inda take da mutum 1,616, sai Abin mai mutum 2,629.
Jihar Borno ce kan gaba a yankin arewacin ƙasar, inda take a masu rajista 296,409, sai jihar Kebbi mai 193, 781, sai Kaduna mai mutum 187,480.
Jihar Kano da ta fi kowace yawan al’umma a arewacin ƙasar na da masu rajista 66,091.
