Gwamnan Kano ya karɓi rahoton kwamitin wayarwa kan rajistar masu zaɓe

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton aiki daga kwamitin da aka kafa na musamman kan wayar da kan jama’a kan rijistar masu zaɓe.

Yayin da yake bayyana gamsuwarsa da ci gaban da kwamitin ya samu zuwa yanzu, Gwamna Yusuf ya jaddada aniyar Kano na ci gaba da zama jiha mai yawan masu rijista fiye da kowace jiha a Nijeriya.

Ya buƙaci mambobin kwamitin da su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa mai cancanta ya yi rajista tare da samun katin zaɓe.

Ya ce an kafa kwamitin ne da gangan domin ɗaya daga cikin manufofin gwamnatinsa na inganta dimokuraɗiyya ta hanyar ƙarfafa shiga jama’a cikin harkokin zaɓe.

Gwamna Yusuf ya tabbatar wa kwamitin goyon bayan gwamnatinsa a kowane mataki na aiwatar da wannan aiki.

Tun da farko, mataimakin gwamnan jiha, Kwamared Aminu Abdussalam, ya shaida wa Gwamnan cewa ya gana da kwamishinan zaɓe na INEC mai kula da Kano, inda suka tattauna kan shirye-shiryen da aka kammala domin tabbatar da gudanar da aikin ba tare da tangarɗa ba. 

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta samar da dukkan yanayi mai kyau da zai taimaka wajen cin gajiyar wannan shiri domin kowane ɗan ƙasa ya samu yin rajista.

Shugaban kwamitin kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya gabatar da bayani kan ayyukan kwamitin tun bayan kaddamar da shi makonni biyu da suka gabata.

Ya bayyana cewa kwamitin ya kai ziyarar ban girma ga kwamishinan INEC domin kafa kyakkyawar dangantaka ta aiki, tare da tabbatar da cewa babu ɗan kasa mai cancanta a Kano da za a bari a bayan wajen yin rijista – ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ko matsayi ba.

Haka kuma, Waiya ya bayyana irin ganawar da suka yi da masu ruwa da tsaki, ciki har da ƙungiyar Mawallafa, inda aka wayar musu da kai kan rawar da za su taka wajen karfafa jama’a su yi rajista. 

An kuma haɗa da ƙungiyoyin farar hula (CSOs) waɗanda aka bukaci su yi amfani da ƙwarewarsu wajen fadakar da jama’a kan muhimmancin yin rijista a matsayin haƙƙi da nauyin ɗan ƙasa.

Bugu da ƙari, ya ce kwamitin ya gana da shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, waɗanda suka yi alƙawarin tallafawa wajen ɗaukar masu sa-kai da za su taimaka a rijistar kan layi a cikin gundumomi 484 na jihar.

Ya jaddada cewa wannan yunƙuri na wayar da kai kan rijista, ya samo asali ne daga kishin kasa da kuma jajircewa wajen ganin an tabbatar da ci gaban Kano.

By ukarofi