
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wani mummunan al’amari ya faru a unguwar Makwarari da ke jihar Kano bayan ruftawar wani ginin sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a yankin.
Al’amarin yayi sanadiyyar mutuwar matar gidan, Balaraba Tijjani mai shekaru 35 yayin da ƴaƴanta guda biyu, Abdulnasir ɗan shekara 11 da Abdallah mai shekaru 13 suka samu raunuka.
An fara ruwan ne a ranar Alhamis inda ya cigaba har zuwa safiyar ranar Juma’a wanda hakan ya sabbaba rushewar gidan.
Baya ga haka ne maƙofta suka garzaya da su asibiti don ba su kulawa inda a nan ne mahaifiyar ta rasa ran nata.
Marigayiyar ta kasance mata ce ga wani Tijjani Magaji, ma’aikacin Ma’aikatar Labarai ta jihar Kano wanda aka tura aiki zuwa Ma’aikatar Matasa da Wasanni a matsayin mai ɗaukar hoto.
A baya kaɗan ne, Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NIMET tayi hasashen samun mamakon ruwan sama wanda ka iya haddasa ambaliya a jihohin Arewa ciki har da Kano inda ta ankarar da al’ummar wasu yankunan su sauya matsugunansu.
