Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Okezie Kalu, ya karɓi sabbin mambobi sama da 3,000 daga jam’iyyun siyasa daban-daban zuwa jam’iyyar APC a jihar Abia a hukumance.
Jaridar ɓanguard ta rawaito cewa an karɓi sabbin ‘yan APC din ne a Akwete da ke Ndoki a ƙaramar hukumar Ukwa ta Gabas a yayin wani shirin bayar da tallafi da Hon. Chris Nkwonta, mamba mai wakiltar Ukwa ta Gabas da Ukwa ta Yamma a majalisar wakilai ya shirya.
Da yake jawabi ga ɗimbin jama’a da ga Ukwa ta gabas da kuma Ukwa ta Yamma, Kalu ya yi ƙarin haske kan cewa akwai arin dubunnai da za su sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, yana mai jaddada tasirin jam’iyyar a yankin.
A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Leɓinus Nwabughiogu, ya fitar, Kalu ya bayyana guguwar sauya sheƙar a matsayin wata alama ta nuna godiya da gamsuwa ga mulkin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da irin tagomashi da Kudu maso Gabas ke samu, musamman ta hanyar kafa hukumar raya Kudu Maso Gabas (SEDC) da ke da nufin ganin an same da ci gaba mai ɗorewa a yankin.
