Matakan yayata ilimin kimiyya na Ƙasar Sin zai amfani duniya baki ɗaya

Daga IBRAHIM YAYA

A kwanakin baya ne mahukuntan ƙasar Sin, suka fitar da wani kundin bayani, mai ƙunshe da matakan yayata ilimin kimiyya tsakanin al’ummar ƙasar, matakan da ake fatan za su taimaka wajen ingiza ƙwazon al’umma a fannin samar da ci gaba ta hanyar yin ƙirƙire-ƙirƙire.

Ofisoshin sakatariyar kwamitin tsakiya na JKS, da majalisar gudanarwar ƙasar ne suka fitar da kundin cikin haɗin gwiwa.

Kundin ya kuma ƙarfafa muhimmancin haɗe matakan yayata ilimin kimiyya, da fannin ƙirƙire-ƙirƙiren kimiyya da fasaha.

Kana ya fayyace sassa daban-daban game da irin matakan da za a aiwatar domin cimma nasarar da aka sanya gaba.

An tsara cewa, ya zuwa shekarar 2025, za a kai ga faɗaɗa ayyukan yayata ilimin kimiyya tsakanin al’umma, inda masu bincike za su kara taka muhimmiyar rawa, wajen yaɗa ilimin kimiyya, ana kuma sa ran adadin al’ummar ƙasar Sin masana ilimin kimiyya zai haura kashi 15 bisa 100, kana adadin ’yan ƙasar masu maida hankali ga kimiyya da Ƙirƙire-ƙirƙire zai yi matuƙar ƙaruwa.

Kundin ya ƙara zayyana cewa, ya zuwa shekarar 2035, ana sa ran adadin al’ummar ƙasar Sin masu sani game da ilimin kimiyya zai kai kashi 25 bisa dari, yayin da yawaitar masu fahimtar kimiyya zai taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantaccen ci gaba.

Abin da ke ƙara bayyana cewa, kimiya da fasahar Ƙirƙire-ƙirƙire sun kasance muhimman tushen ci gaban ƙasa a wannan zamani.

Wannan na zuwa ne, yayin da aka yi nasarar kammala bikin baje kolin cinikayyar hidima na ƙasa da ƙasa na ƙasar Sin na wannan shekara.

Yayin bikin na kwanaki 6, an gudanar da jigon taruka sama da 100 da gabatarwa da shawarwari fiye da 60, wanda ya cimma jimillar nau’o’in sakamako 1,333 da suka haɗa da hada-hadar kasuwanci, da saka jari, da gabatar da dabaru da yarjeniyoyin hannayen jarin Ƙirƙire-ƙirƙire a sauransu.

A bana yawan mahalarta taron ya zarce dubu 250. Saɓanin yadda a mafi yawan lokuta irin wadannan bukukuwan baje ƙolin ke ƙarewa a matsayin wani taro na shan-shayi, bikin CIFTIS na bana, ya zama mafi girma a ɓangaren ma’auni da kimar bunƙasa duniya.

Ya kuma janyo hankalin manyan kamfanoni 507 dake sahun gaba a duniya, inda suka halarci bikin a zahiri.

A karon farko an gabatarwa kamfanoni da cibiyoyi sabbin samfuran fiye da 100 da sabbin fasahohi na nasarori a fannonin kwaikwayoyin tunanin dan-Adam.

Duk da cikas din da ake fuskanta a ƙoƙarin da ake na dunƙulewar duniya gami da rikice-rikice da ake fuskanta a sassan duniya, bikin na CIFTIS ya ƙara samun mahalarta, saboda wasu muhimman dalilai, da suka haɗa da yadda kasuwar ƙasar Sin take jawo hankali sosai, da yadda bikin ya zama muhimmiyar alamar yadda ƙasar Sin take kara buɗe kofa ga kasashen ƙetare, zurfafa hadin gwiwa, da ba da jagora kan yin kirkire-kirkire, da nuna aniyar ƙasar Sin ta kara azama kan ɗinkewar tattalin arzikin duniya, lamarin da ƙasashen duniya ke matukar buƙata yanzu.