Ranar Hausa Ta Duniya: An bar jaki, ana dukan taiki

Daga RABI’U NA’AWWA

Hausa harshe ne da Allah ya tarfa wa garinsa nono. Bisa wannan dalilin likkafarsa sai ta ci gaba ta yanda ya zamto mesa mai haɗiye dukkan wani ɗan ƙaramin yare da ya kusance shi ko maƙwabtaka da shi.

Sai dai kash! Mafi yawan al’umar da Allah ya mallaka wa wannan harshe bisa ga dukkan alamu, suna yi masa riqon sakainar kashi. Ko kuma mu ce, sun bar jaki ne sun kama dukan taiki.

Misali, mu ɗauki harshen Swahili, wanda yake harshe na farko a Afrika da aka ce ya kere harshen Hausa a yawan masu magana da shi. A zahirin gaskiya idan aka tsananta bincike, abin ba haka yake ba.

Gata ne kawai daga al’ummar wannan harshe da ya samu shi ne dalilin da ya sa ya samu wannan tagomashi. Saboda al’ummar da suke da wannan yare sun tashi haiƙan wajen inganta shi da ilminsu da ƙarfinsu, da kuma kuɗaɗensu, sannan kuma sun fi Hausawa tallata shi a kasuwar Duniya.

Bisa wannan dalilin ne ma ƙungiyar gamayyar Africa ta (AU) a taron shugabannin ƙasashe da ta yi kwanan nan, ta ɗauki harshen na Swahili a matsayin harshen aiki na hukuma a ƙasashen Afirka.

Har’ilayau, Swahili shi ne harshen hukuma na Ƙungiyar Ƙasashen Gabashin Afirka (EAC). Duk wannan tagomashin ya samu ne sakamakon kula da Harshen yake samu daga Al’ummar wannan harshe.

Na taɓa hira da wani Farfesa da yake a wata babbar Jami’a a Sudan, ya ke cewa, “Da a ce za a raba adadin kuɗin da ake kashe wa harshen Swahili gida biyu a kashe wa Harshen Hausa waɗannan kuɗaɗen, da babu wata ƙasa a Duniya da za ka je ba ka samu masu jin harshen Hausa ba.

To amma kamar yanda na faɗa a baya, harshen Hausa ba ya da wani gata da yake samu daga Al’ummarsa. Harshe ne da ya zamto zaki mai kashe wa kansa da kansa nama; su kuma al’umar tasa sun bar jaki sun koma suna dukan taiki. Dalilin a nan shi ne:

A kaf al’ummar Hausawa kama daga kan iyayen ƙasa Sarakuna, zuwa kan Attajirai da Malaman Jami’a da ƙungiyoyi masu zaman kansu, zuwa kan ɗaliban ilmi, kowa ya karkata kansa zuwa wani bigire daban ba wanda ya dace a ɗora wannan harshe ba. Misali:

Sarakunanmu na Hausawa tun bayan da Fulani suka zo da sunan Jihadi suka ƙwace mana masarautunmu, suka rusa wasu daga cikin al’adunmu, daga wannan lokacin babu wani yunquri da suka sake na tunanin bunƙasar wannan harshe, su kuma sauran Masarautun Hausawa da suka rage, maimakon sauran Hausawan su agaza musu a samu wata ƙasaitacciyar Daula da za ta zama jagoran dukkan Hausawa a ko’ina suke, su ma sai aka rufe masarautun a gefe. Haqiqa wannan babban ƙalubale ne ga al’umar Hausawa.

Idan ka ɗauki Attajirai, su kuma bama a maganar su. Saboda in dai a maganar Harshen Hausa ce, tuni suka tsuke bakunan al’jifansu, babu mai iya cire wasu maƙudan kudi don tallata wannan harshe a Duniya. Amma suna iya zuba jari a wasu ƙasashe da za a iya amfani da su don tallata nasu harsunan. Bahaushe kenan, mai ban haushi!

Sai Malaman Jami’a, su waɗannan ana kallonsu ne tamkar madubi ko fitilar dake haskaka sauran al’umma, amma abin takaici sun harɗe hannuwansu a kan kirji. Sai dai idan sun ga wani ya yi wani yunƙuri cikin Fasihan da suke ɗan ƙoƙari a kan harshen kamar ‘yan jarida ko marubuta da masu wasan kwaikwayo da makamantansu, maimakon su dafa su gyara musu su dawo da su saiti idan sun yi ba dai dai a tafiya ba; a’a, sai dai su koma gefe suna faman suka suna an yi kaza da kaza. Kamar yadda yake faruwa a yanzu tsakaninsu. A matsayin masu ruwa da tsaki na al’adu, Marubuta, ‘yan fim, ‘yan jarida da sauransu.

Idan muka dawo a kan maganar ranar Hausa ta Duniya, har yanzu da nake wannan magana wannan ranar bata tabbata ba a hukumance. Saboda akwai ƙungiya da ita ce ke da alhakin tabbatar da wannan rana ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya wato UNESCO, kuma har yanzu wannan ƙungiya bata tabbar da ita ba, saboda babu wata hanya sahihiya da aka bi don tabbatar da hakan.

Wannan laifin shi ma na fi dora shi a kan malaman Jami’a da sauran ɗaliban al’ada, saboda su sun san hanyoyin da ya kamata a bi don samun tabbatacciyar rana.

To saboda rashin yin hakan ya sa su ɗaliban Hausa suka ga rashin kyautawar ta yi yawa shi ya sa suka zavi wannan rana ta 26 ga watan Agusta ta zama ranar Harshen Hausa ta Duniya.

Kuma duk da haka yau shekara bakwai kenan ana gabatar da bukukuwan wannn rana amma har yanzu ba a yi binda ya dace don tabbatar da wannan rana ba. Maimakon idan an zo bikin a fitar da muhawarorin da suka shafi tallata harshen a kasuwannin Duniya ta hanyar da ta dace, sai ka ga an mayar da hankali wajen karin magana, tatsuniya da makamantansu, tamkar su ne kawai matsalolin harshen.

Idan ka koma ga ƙungiyoyin da suke kiran kansu na Hausawa, da ka huda su babu abinda za ka tsinta face faɗan cikin gida, ko na neman muqami. Yayin da wasu suka ja tunga a kan ba za su yi tafiya da kowa ba, sai tsantsar Bahaushe ba surki, wasu kuma sun fi mayar da hankali a kan zumunta, kai wasu ma idan ka fassara su ba su dace da kowane irin suna ba face ‘yan damfara.

Dalili shi ne, sun zo sun naɗa kansu sarautu na ba gaira ba sabab, ba su tsinana komai sai bin masu hannu da maiƙo su kwaɗaita musu cewa za su basu sarauta ta Hausawa, su karɓi kuɗinsu su yi musu naɗe-naɗen banza marasa tushe. Bisa waɗannan dalilai ne ya sa na ce, an bar jaki, ana dukan taiki.

A ƙarshe, kirana ga wannan al’umma mai albarka shi ne: A samar da wani kwamiti mai ƙarfi da zai tuntuɓi ƙungiyar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da al’adu a kan samar da tabbatacciyar ranar Hausa ta Duniya.

Samar da wani kwamiti da zai hadar da masu ruwa da tsaki a kan al’adu da suka haɗar da: Sarakunan gargajiya da masana da ɗaliban ilmi, da ‘yan jarida, da marubuta da kuma masu wasan kwaikwayo sai Gwamnati tare da ƙungiyoyi masu zaman kansu, da za su fito da hanyoyin da za a bi wajen tallafa wa harshe da suka yi dai-dai da cigaban Zamani (Sustainable Development Goals) a fitar da tsare-tsare da kuma hikimomin fasahar zamani da za a bi wajan tallata wannan ƙasaitaccen harshe da bunƙasarsa.

Ko kuma mu ɗauki misali da matakin da Gwamnatin Tanzania ta ɗauka wajen tallata nata harshen, inda Gwamnati ta shiga, cikin hanyoyin da ta bi akwai kafa cibiyoyin bincike a kan harshe, samar da jami’ai ta musamman da za su kula da shirin a fannoni daban-daban.

Wato, kamar girka kevantattun kalmomi (terminologies), shirya ƙamusoshi (lexicography), da nahawu, samar da rubuce-rubuce ga makarantu na musamman da wallafa litattafai kan fannonin ilmi daban-daban, kyautata hulɗa a tsakanin kasashen da suke da masu magana da yaren.

Sai kuma shirya bita ta auna nasara ko naƙasu a kai-a kai, da makamantansu. Ire-iren waɗannan hanyoyi ne ya kamata a mayar da hankali idan ana son cigaban wannan harshe namu. Allah ya dafa mana.

Rabiu Na’auwa ya gabatar da wannan takarda a fadar Mai martaba Sarkin Damagaram a bikin ranar Hausa ta Duniya, 26 ga Augusta, 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *