An tsare Tukur Mamu da matansa a Masar

Daga BASHIR ISAH

An tsare mawallafin nan wanda ke shiga tsakani wajen kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasan hanyar Kaduna-Abuja da aka yi garkuwa da su, Tukur Mamu, a ƙasar Masar.

An tsare Mamu ne a ranar Talata a Babban Filin Jirgin Saman Alƙahira a daidai lokacin da yake shirin tafiya Saudi Arebiya.

Mamu, shi ne mawallafin jaridar nan ta Desert Herald, kuma mai magana da yawun fitaccen malamin Islaman nan na Kaduna, Ahmad Gumi, ya taka rawa wajen kuɓutar da wasu daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna a watan Maris da ya gabata.

Sai dai, Mamu ya shaida wa jaridar Premium Times a safiyar Laraba cewa, an maido da shi Nijeriya bayan jami’ai sun yi masa tambayoyi ba tare da samun sa da wani abu da ya saɓa wa doka ba.

An tsare Mamu ne tare da matansa biyu da wani mutum guda wanda bayanai suka nuna sun bar Nijeriya ne don zuwa Umarah a Saudiyya.

Ana sa ran isowarsu Babban Filin Jirgin Saman Aminu Kano da ke Kano ranar Laraba wanda mai yiwu ya sake faɗawa hannun jami’an DSS don ci gaba da amsa tambayoyi.

Mamu ya sanar da janyewarsa wajen ci gaba da shiga tsakani wajen kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da ke hannun ‘yan bindiga bayan da ya yi zargin gwamnatin Nijeriya na yi wa rayuwarsa barazana.