Daga AMINA YUSUF ALI
Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Barkanmu da haɗuwa a wani makon.
A kwanakin baya mun tattauna a kan yadda maza za su fuskanci yaren mata a soyayya. Ba wani yare ne can daban ba kamar Yarbanci ko Turanci ba fa.
Amma yare ne na fahimtar ɓoyayye da bayyanannen saƙon da jinsin macen yake isarwa ga jinsin namiji ko kuma fahimtar halayyarta don samun sadarwa mara sarƙaƙiya. Kuma meye amfanin samun sadarwan mai sauƙi?
Sai don a samu zaman lafiya da fahimtar juna a zaman aure. Ma’aurata duk yadda za su yi wa kansu da kansu ƙarya a kan farin cikinsu, dole farin cikinsu yana da alaƙa ta ƙus da ƙus da irin zaman da suke yi da iyalinsu.
Hasali ma fiye da kaso 80 na samun kwanciyar hankalinsu ya dogara kacokan a kan samun nutsuwar abokin zamansu. Idan mace ba ta jin daɗin zaman aure da kai, kai ma ba ka isa ka ce za ka kasance cikin farin ciki ba.
Haka idan namiji shi ma ba ya jin daɗin aurensa, matarsa ba ta faranta masa, to labudda ba zai taɓa samun nutsuwa isasshiya ba. Hakazalika, dan mace ba ta faranta wa miji shi ma sai ta yi ta ƙoƙarin cuzguna masa, kamar ƙin yi masa biyayya, hana shi haƙƙoƙinsu kamar girki, shimfiɗarsa da sauransu don kawai ta ƙuntata masa.
Mace kuma idan namiji bai jin daɗin zama da ita, to shi ma sai ya ɗauki nasa salon. Ko ya hana ta haƙƙoƙinta da suka shafi kuɗi, ko ya dinga ƙaurace mata da gidan ma gaba-daya idan ya ga dama, haka dai.
To ashe kenan kowanne ɓangare ana buƙatar a kyautata masa don kai ma ka samu kwanciyar hankali, wanda shi ne ladanka. Amma ta yaya za a kyautata wa wanda ba a fahimci ma me yake ko take buƙata ba?
Kuma ta yaya za a fahimta ɗin? To a nan maganar fahimtar yaren juna ta fito. Don ba zai yiwu ka yi wa mutum magana da yaren da sam ba ya fahimta, da shi da shiririta duk ɗaya. Sai ka je ka yi ilimin nasa yaren sannan ka zo ka yi masa magana ya san me kake cewa.
Kuma samun nutsuwar ƙwaƙwalwa ya ta’allaƙa ga farin cikin da mutum yake samu. Ko ma dai yaya ne, fahimtar yaren namiji yana da matuƙar muhimmanci ga mace kamar yadda ita ma fahimtar nata yake gare shi. Haka sanin yaren juna zai sa a ƙara fahimtar mutum a dinga masa uzuri. Kuma duk dai zaman lafiya ake samu idan an yi haka.
Abu na farko da mace ya kamata ta fuskanta shi ne, ita mace yadda ta iya soyayya take iya nunawa ta ɓangarenta to ba lallai ne shi ma namiji hakan zai nuna ba. Yadda Allah ya halicci jinsunan guda biyu daban-daban, haka ya halicce su da ɗabi’u daban-daban.
Don haka, ba qaramin kuskure ne da yaudarar kai ba ne ki yi tsammanin yadda kike nuna soyayyarki ya zama dai-dai da yadda namiji ke nuna tasa. Ita mace ta fi namiji nuna matsananciyar kulawa a soyayya.
Amma shi namiji ba a sau nawa ya kira ki a waya ko ya yi miji kalaman soyayya za ki gane yana sonki ba ko a’a. Shi soyayyarsa, tausaya miki, ba ki kariya, ɗaukar nauyin ki, damuwa da dangin ki da girmama iyayenki da makamantansu.
Ba kullum kawai ya gaya muku kalaman soyayya ko rungume-rungume ba. Idan wannan kike so, ki kalli fim ɗin indiya ko na Amurka ko makamantansu. Ko kuma ki karanta littafan ƙagaggun labarai. Kuma ki sani, halinsa ne, ba wulaƙanci ba ne.
Sannan wani misalin shi ne, mace tana so namiji ya dinga ɗan taimaka mata da aikin gida don tana gani wasu ƙawayenta ko wasu ƙabilun suna yi. Abinda ba ki sani ba shi ne, su ƙabilun da kike son kwaikwayo yadda suke kashe mu raba a ayyukan gida haka suke yi a ɗaukar nauyin gida ta fuskar kuɗi.
Don haka, matar Bahaushe ba ki da bakin magana a nan. Idan mai sha’awar tayin ne, ko aikinsa ba yawa zai iya. Amma fa don bai taya ki ba, ba ya nufin ba ya sonki ba ne, face sai don ɗabi’arsa ce hakan. Idan kin gane hakan, kin huta.
Hakazalika, ya kamata mace ta sani, shi wannan miji nata yana da nauyin iyali da iyaye da makamantansu. Ba zai yiwu a ce dole wai sai ya dinga katse aikinsa yana kiranki a waya ko ya dawo gida don kasancewa da ke ba.
Aikin nan yana da matuƙar muhimmanci wajen samar muku kwanciyar hankali da nutsuwa da ke da yaranku. Kuma wasu lokutan ma idan suna aikin ke kina gida ba ki san irin ƙalubalen dake gabansa ba.
Don Allah ‘yaruwa kada sana’arsa ta zama abin rigima tsakaninmu. Kaso 90 na sana’ar don ku yake yi. Kuma kira ba dole ba ne idan yana aiki. Idan ya kira sau ɗaya ma ya isa. Idan ma bai kira ba bai yi laifi ba. Sai dai idan yana da wani saƙo da yake son isar miki.
Idan kin kira ne dai bai ɗauka ba ko ya ƙwale ki kuma wannan bai dace ba. Haka idan ba ya dawowa da wuri kamar mijin ƙawarki ko mawabciyarki, to ki sani, kowa da lokacin aikinsa da nasa ra’ayin kuma.
Sannan akwai maganar fushi da namiji yake yi. Su Maza yawanci fushinsu sukan huce ne a kan wani abu saɓanin maƙasudin abinda ya assasa musu ɓacin ran.
Kuma mafi yawancin lokuta ke matarsa saboda kina tare da su, kanki ake sauke wannan vacin ran, kamar yadda idan daɗin ne ma ke kike riga kowa samu.
Misali; idan ba shi da kuɗi kan matar zai sauke bala’in, haka idan ma wani ne ya ɓata masa a waje ko danginsa, ko ma wasu matan nasa, wacce ya zo wajenta ita zai sauke wa.
Sai ya ƙirƙiro faɗa da takale-takale. Wani lokaci sai ki yi ta zargin kanki da kanki ko wani abu kika yi ko kuma ki biye masa ku haura. Ki rabu da shi ya yi ya gama. Idan ya huce a wancan fushin nadama ce take rufe shi.
Bugu da ƙari, mata suna ganin kamar miji idan ba ya hira da su ba ya son su ne. Kamar ba ya yarda a yi gulmar kishiya ko danginsa. Shi wani namijin haka Allah ya yi shi. Kamar yadda na faɗa a baya, halittar jinsin mace daban da namiji.
Ba kowanne namiji ne ya iya gulma ba. Idan miji ko bai iya ba kada ko koya masa dole sai ya yi gulmar kishiya ko danginsa sannan za ku zauna lafiya.
Mafi yawancin abubuwan da zai faɗa Miki ba gaskiya ba ne illa don kunnenmu ya ji abinda yake son ya ji. Kuma wani yana tsoron Allah kuma yana gudun fitina. Wanda kuma ya biye mace, ba zai ga dai-dai ba a Duniya da lahira ba. Allah ya kiyashe mu.
Wani abu kuma, mace kada ta ɗauka don namiji yana yi wa iyaye ko danginsa abu wai kamar ita ba ya son ta ne. A’a, ƙoƙari yake ya sauke haƙƙoƙin Allah a kansa.
Idan Allah ya ba ki irin wannan mijin ma, ya ba ki mutumin kirki. Kuma ke ma watarana uwar miji ce za ki fahimci hakan.
Sannan abinda ya kamata mace ta ƙara fahimta shi ne, namiji a halittarsa yana da izza da tsananin sarauta sai dai wasu lokutan yakan danne su. Idan har ba ta ba shi wannan girman da yake ganin ya cancance shi ba, to sai ya yi ƙoƙari ya ƙwata ko ta halin yaya ne.
Akwai abubuwan da za ki ga ba wani abu ba ne idan kin yi masa. Saboda ko ke aka yi wa ba za ki ji komai ba. Amma shi a wajen namiji kin raina shi ne. Wani namijin dai dai da soyayya kika nuna masa gani yake kin raina shi.
Irin zolayar nan ma ta masoya ba safai ya fi so ba. A wajen namiji dukkan abinda ba ya so idan kika kuskure ko da yaya ne, kin raina shi. Don haka bin doka sau da qafa ya kama ki. Haka kada ma ki fara zancen wani namijin a gaban mijinki ko saurayinta musamman idan wanan mutumin ya fi mijin baki ko saurayin naki wasu abubuwan.
Don haka, mata sai a kiyaye. Kada ku mu’amalanci mazajenku da mua’amalar da kuke yi wa mata ‘yanuwanku. Ku mu’amalance su a matsayin shugabanni. Kuma ko ba komai da ma haka musulunci ya tsara kuma ya yi umarni.
Mace ta yi biyayya ga mijinta ko da ya kasance ta fi shi daraja ko mulki ko dukiya. A nan za mu tsaya. Amma yarukan namiji da mace take buƙatar fahimta suna da yawa sai a ɗora bincike daga inda muka tsaya.
Domin mazajen ma a tsakaninsu sun banbanta da juna. Kowa da irin yarensa. Saboda haka, sai ki karanci yaren mijinki, ki biya, ki haddace kuma ki iya don ki dinga fahimtar saƙonninsa.
Ko ba don komai ba, don a zauna lafiya ki dinga samun abubuwan da kike so a wajensa. Sannan ku samu zaman lafiya a gidan aure.
Sai wani makon idan Allah ya kai ranmu.
