‘Yan wasan fim biyar da suka fi arziki a duniyar finafinai

Daga AISHA ASAS

Bincike ya tabbatar cewa, ba waɗanda suka fi samun roman aikinsu a duniyar nishaɗantarwa kamar masu harkar fim da kuma masu buga wasan ƙwallo, hakan ya biyo bayan irin so da ƙaunar da mutane ke yi wa wannan ɓangare guda biyu.

Sanannen abu ne, mutane mafi rinjaye na duniya na sha’awar kallon finafinai, walau waɗanda ake yi a yarensu ko na wasu al’ummar. Wannan ne ya sa harkar fim ta zama cikin jerin farko da ke samar da kuɗin shiga da kuma samar da aikin yi ga mata da maza musamman ma matasa, musamman a vangaren jarumai, ba don komai ba kuwa sai don ba wa masu kallo abinda suke buƙata.

Idan muka yi zancen jarumai dole mu kawo masu kallo, domin ba jarumin da zai zama babban jarumi, ya ci moriyar harkar, face da taimakon masu kallo, asalima duk wanda ya zama babban jarumi masu kallo ne suka kaishi matsayin, domin sai sun nuna ka ne za ka yi shuhura. A taƙaice dai manyan jarumai da bazar masoyansu suke taka rawa. Kuma su ne silar duk wani alheri da za su samu a harkar. Ta yaya?

A lokacin da ka fara fitowa harkar fim, yawan masu son ganin finafinanka, yawan yadda masu shirya finafinai za su nemi yin aiki da kai, ma’ana dai ana amfani da buƙatar masu kallo kan fuskokin da suka fi so wurin haska masu finafinai, ba don kamai ba, sai don fatan ya samu karɓuwa.

Abin lura a nan shine, yawan masoya finafinan da jarumi ke yi na kai shi ga samun kuɗi fiye da waɗanda ba su kai shi masoya ba, ta hanyar sanya shi a finafinai da yawa, kuma kamar yadda muka sani mai kaɗan bazai taɓa zama ɗaya da mai yawa ba.

Abu na biyu da masoya za su iya ba wa jarumi shine, suna a idon duniya, wanda wannan sunan zai iya kai shi ga samun alkhairai masu yawa, kamar tallata hajoji ko kamfani ko wasu wayar da kai na wasu ƙungiyoyi ko gwamnati da sauransu, kuma duk waɗannan harka ce ta samun kuɗi.

Da waɗannan misalai biyu mai karatu zai iya amincewa a harkar fim dole ne kamar kowacce sana’a wani ya fi wani samu.

Don haka ne shafin nishaɗi na wannan mako ya kawo wa mai karatu jarumai biyar da suka fi kwankwaɗar romon aikin na su, don su tabbatar da bayanin da muka yi a sama:

Jerry Seinfeld

Jerry Seinfeld: Jarumi Jerry Seinfeld ɗan asalin Ƙasar Amurka ne, jarumi ne a masana’antar finafinai ta Hollywood, wanda ya fi ƙarfi a wasannin barkwanci. Ƙiyasin dukiyarsa kuwa, Dalar Amurka miliyan 950. Da wannan ne Jerryya zama mafi arziki a cikin jarumai na duniya.

Tyler Perry: Tyler Perry shima dai ɗan Ƙasar Amurka ne, kuma shine jarumi na biyu a jerin jarumai mafi arziki na duniya, kasancewar dukiyar da yake da ita wadda ta kai Dala miliyan 800.

Shah Rukh Khan

Shah Rukh Khan: Ɗan wasan kwaikwayo a masana’antar finafinai ta Indiya, wato Bollywood, Shah Rukh Khan, wanda ake wa laƙabi da Sarkin Bollywood (King of Bollywood) ya shigo a lissafin na mu a matsayin na uku a arziki sakamakon dukiyarsa da ta kai Dala miliyan 770.

Tom Cruise

Tom Cruise: Ɗaya daga cikin jaruman da suka fi tsada a duniya, ba’amurke ne kuma mai shirya finafinai. Tom ya zama na huɗu a lissafin na mu ne da Dalar Amurka miliyan 600 da ya mallaka.

Jackie Chan: Ɗan wasan da aka fi sani a finafinan Chana musamman ma na faɗa irin na su. Sai dai tafiya da ta yi tafiya Hollywood ta zama gida ga wannan jarumin. Jackie Chan ɗan Ƙasar Chana ne da ya shigo harkar fim tun yana da shekaru biyar a duniya.

Jackie Chan

Mawaƙi ne, kuma mai rubuta wa da shirya finafinai. Ƙiyasin dukiyarsa kuwa Dala miliyan 520, hakan ya ba shi damar zama na biyar a jerin jaruman da suka fi kudi na duniya.