An shirya tattaunawar Tiangong tsakanin ‘yan sama jannatin Sin da matasan Afirka cikin nasara

Daga CMG HAUSA

An yi nasarar shirya tattaunawar Tiangong wato cibiyar nazarin sararin samaniya ta ƙasar Sin, tsakanin ‘yan sama jannatin dake kumbon Shenzhou-14 da wakilan matasa da yaran ƙasashen Afirka cikin nasara jiya Talata.

Ban da babban wurin da aka keɓe a hedkwatar ƙungiyar tarayyar Afirka wato AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin ƙasar Habasha, an kuma keɓe wasu wuraren tattaunawa a ƙasashen Afirka guda 8 waɗanda suka hada da Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar.

Jakadan ƙasar Sin dake Nijar Jiang Feng, ya gabatar da wani jawabi a wurin tattaunawar da aka keɓe a ƙasar, inda ya bayyana cewa, akwai dadadden zumunci tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka, kuma tattaunawar Tiangong da aka shirya, ta kara haɓaka cudanyar dake tsakanin sassan biyu.

Ko shakka babu tattaunawar za ta zaburar da nazarin sararin samaniya na matasa da yara na ƙasashen Afirka.

A yayin taron, wakilan matasa da yaran ƙasashen Afirka sun kalli faifan bidiyon tattaunawar da aka gabatar, tare da nuna mamaki matuƙa da irin fasahohin zamani game da nazarin sararin samaniya na ƙasar Sin da babban sakamakon da ta samu a ɓangaren da suka gani.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa