Matar Abdulmalik Tanko da ake zargi da kisan Hanifa, ta nemi mijin ya sawwaƙe mata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Matar Abdulmalik Tanko wanda ake zargi da garkuwa da kuma kashe Hanifa a Jihar Kano, Jamila Muhammad Sani, ta ce tana son mijin nata ya rubuta mata takardar saki.

A jiya Juma’a ne dai aka gurfanar da Jamila, mai shekara 30 da haihuwa a Kotun Majistare 12 da ke zamanta a Gidan Murtala, bisa zargin haɗin baki da ita a ɓoye Marigayiya Hanifa.

Gurfanar da Jamila ɗin ya zo ne bayan da a ranar Alhamis ta bayyana a gaban Babbar Kotun jiha 5, a bisa jagorancin Mai Shari’a Usman Na-abba, ta bada shaida a kan yadda Tanko ya kawo Hanifa gidansa har ma ya yi ƙaryar cewa mahaifiyar yarinyar ce ta yi tafiya zuwa Abuja.

Sai dai kuma da aka gurfanar da Jamila a gaban kotun, alƙalin kotun, Muhammad Jibril, ya wanke ta ya kuma umarci da a sake ta daga inda ake tsare da ita tun lokacin da aka kama mijin nata.
Da take zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, Jamila ta gode wa Allah bisa wanke ta da Ya yi, kuma ta ji daɗi a bisa hukuncin na kotu.

A cewar ta, ita yanzu tana neman Tanko ya sake ta saboda ba za ta iya zaman dakon jiran sa ya fito ba.

“Ni da har yanzu da ƙuruciya ta. Ba zan iya zaman jiran sa ba. Ni kawai ina neman ya sake ni in je in samu wani mijin na aura. Ni ba zan iya zaman dakon jiran sa ba,” inji Jamila.