Matasa 11,000 aka ba takardar aiki a gwamnatin Abba – Sunusi Kwankwaso  

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso, Mai Ba Wa Gwamnan Jihar Kano Shawara Kan Harkokin Siyasa, ya bayana cewa, ko yanzu gwamnatin Abba ta biya bashin alƙawura da dama da ta ɗauka a lokacin gangamin yawon neman ƙuri’ar jama’ar Kano a jam’iyyar NNPP a wani jawabi da ya gabatar a birnin Kano a makon da ya gabata.

Sunusi Kwankwaso, ya ƙara da cewa matasan da suka samu aiki suna da yawa a Kano waɗanda aƙalla matasa maza sama da 11,000 suka samu takardar aiki haka abin yake wajen bai wa mata da dama suka sun samu takardar aiki na dindindin a Gwamnatin Abba, a fannoni daban-daban da suka haɗa da fannin lafiya, ilimi da sauran fannoni na ci gaban al’ummar Kano.

Ya ce kuma wannan gwamnati ta ba mata sama da dubu 10 tallafin Naira dubu 50 a wata biyu tak da fara ba su wanda kuma za a ci gaba duk wata za a ba mata sama da dubu biyar duk wata har ƙarshen lokacin gwamnatin Abba na shekara 8 in Allah ya so.

Kazalika ya ce babban abinda wannan gwamnati take buƙata shi ne addu’ar tabbatar da zaman lafiyan Kano da Nijeriya baki ɗaya musamam ganin yadda gwamnatin Allah ke taimakon al’umma ta kowane fanni, inda ya ce hakan na ƙara baƙantawa maƙiyan Kano da al’umarta rai. “Don haka kullum burinsu a samu akasin nasara a wannan gwamnati amma da taimakon Allah da addu’ar al’ummar Kano da Nijeriya, kullum gwamnatin Abba, nasara ta ke samu wajen ciyar da Kano gaba a kowanne fanni na rayuwar al’umma.

A ƙarshe Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso, ya yaba wa Gwamnan Kano kan yadda ya tashi tsaye wajen tunkarar matsalolin cikewar magudanan ruwa da ka iya haddasa mummunan ambaliya kamar yadda aka yi hasashe a wannan damina da dai sauran matsaloli da suka addabi Kano da ya sa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya cikakken bacci sai ya ga ƙarshen matsalolin Kano da Kanawa.

By ukarofi