’Yan sanda sun kashe shugaban ƙungiyar asiri da ya kashe DPO a Ribas

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta ce gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, ya cika alƙawarinsa na biyan la’adar Naira Miliyan 100 kan wani fitaccen shugaban ƙungiyar asiri, Gift Okpara, wanda ake kira 2Baba, wanda tare da ‘yan ƙungiyarsa suka kashe wani jami’in ‘yan sanda, Sufeto Bako Angbashin, a yankin Oduemude na jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olatunji Disu, ya tabbatar da faruwar lamarin a yayin wani fareti da aka gudanar don karrama jami’in da aka kashe a hedikwatar ‘yan sandan jihar a ranar Asabar, inda ya ƙara da cewa an sako gawar ɗan sandan da aka kashe ga iyalan.

Disu ya ce, “A ranar 25 ga Maris, 2024, ‘yan sanda sun kashe shugaban ƙungiyar da ake nema ruwa a jallo, a wani samame da suka kai maɓoyarsa a unguwar Idu-Ekpeye da ke Ahoada, yayin da aka tsinto gawarsa kwanaki kaɗan a dajin Ibrass da ke yammacin Ahoada, ƙaramar Hukumar Jihar.

“Ina miƙa godiyata ga Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, wanda ya cika alƙawarinsa, ya kuma ba da miliyan N100 ga waɗanda suka bayar da sahihan bayanai da suka kai ga kashe wanda ake zargin, 2Baba, tare da kwato gawarsa, wanda ‘yan ƙungiyarsa suka ɓoye. Ina kuma miƙa godiyata ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, saboda kwarin gwiwa da goyon bayan da ya bayar a tsawon wannan aiki.”

“Shi Angbashin ya taka rawa wajen damƙe hamshaƙin ɗan kasuwa Boboski, wanda ya addabi masu ababen hawa a kan titin Akwa-Ibom na titin Gabas zuwa Yamma, ya kuma maido da zaman lafiya a Bori da kewaye ta hanyar kawar da duk wani nau’in aungiyar asiri a lokacin da yake riƙe da madafun iko, Jami’in ’yan sanda reshen Bori.”

Disu ya ce, kwarjinin Angbashin da kwarewar aiki ne ya sa aka koma da shi sashin Ahoada, inda aka ɗora masa alhakin kama 2Baba.

Ya ce, “Ya yi amfani da duk kwarewarsa wajen damƙe 2Baba da abokansa a raye kuma yana kan hanyar samun nasara a lokacin da ya haɗu da muguwar al’amarin da ya yi sanadin kashe shi tare da yanke masa jiki.

“Bayan faruwar lamarin, rundunar ta kasa gano gawar marigayi SP Bako Angbashim. Duk da haka, a yanzu muna farin cikin sanar da cewa mun samu nasarar kwato gawarsa.”

Da yake karɓar akwatin da ke ɗauke da gawar DPO, yayan marigayin, Dogo, ya nuna farin cikinsa da yadda ɗan uwansa ya yi wa ƙasa hidima a matsayin ɗan sanda na ƙwarai. 

By ukarofi