Matasan Yobe sun tara miliyan N188 domin tallafa wa Ahmad Lawan a takarar gwamna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wata ƙungiya mai suna Coalition of Yobe-East Progressiɓe Youths ta tara jimillar Naira miliyan 188 domin tallafawa burin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, na tsayawa takarar gwamnan Jihar Yobe a zaɓen 2027.

Shugaban ƙungiyar, Dakta Yerima Goni, ne ya bayyana hakan a wurin taron tara kuɗin da aka gudanar a ranar Litinin a Damaturu.

Goni ya ce manufar wannan shiri ita ce ƙarfafa shigar matasa da sauran masu ruwa da tsaki cikin harkokin siyasa da shugabanci.

A cewarsa, an samu kuɗin ne ta hanyar alƙawuran bayarwa, tura kuɗi ta banki da kuma gudunmawar kuɗi kai tsaye.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar na da aniyar ci gaba da inganta shugabanci nagari da kuma ƙarfafa rawar da matasa ke takawa a harkokin jagoranci.

An kuma bayyana cewa taron ya samu halartar matasa da dama, shugabannin al’umma, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar.

Da yake jawabi, Sanata Ahmad Lawan ya nuna godiyarsa bisa wannan yunƙuri, yana mai cewa hakan alama ce ta kishin ƙasa da kuma nagartaccen ɗabi’ar ɗan ƙasa.

Ya ce gudunmawar da aka bayar na nuna yadda jama’a ke da sha’awa da kuma himma wajen shiga cikin harkokin siyasa daga tushe.

Sai dai Lawan, wanda har yanzu bai bayyana a hukumance cewa zai tsaya takarar gwamna ba, ya nuna cewa yana da shirin amsa kiran al’umma domin yi musu hidima.

Ahmad Lawan ya taba zama Shugaban Majalisar Dattawa na 14 daga ranar 11 ga Yuni, 2019 zuwa 11 ga Yuni, 2023, inda ya jagoranci Majalisar Tarayya ta 9 bayan ya gaji Bukola Saraki, kuma daga baya Godswill Akpabio ya gaje shi.

By ukarofi