Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, reshen jihar Kwara sun kama wani mutum mai suna Sylvester Enemo da zargin kashe wata mai ciki Esther Enemo a Ilorin babban birnin jihar.
Rahotonni sun ce matashin mai shekara 29 ya daddatsa gawar matar mai shekara 39 ne, wadda kuma aka ce matar ɗan uwansa ce, bayan ya halaka ta a unguwar Temidire ranar Laraba.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa mijin matar ya yi tafiya a lokacin da lamarin ya faru.
“ƙarin bincike ya sa an gano sassan jikin matar da aka zuba a wani buhu kuma aka jefar a ƙarƙashin wata gada,” a cewar sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta fitar.
Ta ƙara da cewa, jami’anta sun kai gawar Esther asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin.
