Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur da dizal

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Matatar Mai ta Ɗangote ta rage farashin fetur da N100, inda ya sauka daga N1,175 zuwa N1,075 akan kowace lita.

Haka kuma farashin dizal ya ragu da N190, daga N1,620 zuwa N1,430 kan kowace lita.

Hakan na zuwa ne bayan saukar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, wanda da fari ya haura sakamakon rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Masana na ganin matakin na iya kawo ɗan sauƙi ga ‘yan kasuwa, yayin da ake sa ran hakan zai iya sa farashin mai a gidajen mai ya ragu a faɗin Nijeriya.

Matatar ta nuna cewa farashin da ke kan ganga ba ya haɗe da kuɗin da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ke biya.

By Babaji