Farashin mai ya karye a duniya bayan Trump ya ce yaƙin Iran ya ƙare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Farashin mai ya sauka cikin sauri bayan ya yi tashi gwauron zabo duniya suka samu tashin gwauron zabo yayin da Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa yaƙin da ƙasarsa ke yi tare da Isra’ila akan Iran ka iya ƙarewa da wuri fiye da yadda aka tsammani.

Trump ya ce wannan ci-gaba na iya rage fargabar da ke damun kasuwanni a duniya, inda hakan ya sa masu saka jari suka fara mayar da hankali kan damar samun riba a kasuwannin hannun jari.

Wannan yanayi ya kawo kwanciyar hankali a wasu ɓangarori na tattalin arziki, musamman ga masu sha’awar saka hannun jari a fannin makamashi da kasuwancin kayayyaki.

Masana tattalin arziki sun ce duk da wannan ci-gaba, kasuwanni na iya cigaba da kasancewa cikin shiri, saboda yanayin rikicin na iya sauyawa a kowane lokaci.

Kalaman na zuwa ne jim-kaɗan bayan Trump ya bayyana cewa yaƙin ya kusa kammala a wata tattaunawa ta waya da shugaban Rasha, Vladimir Putin, wadda ta ɗauki kusan sa’a guda.

Trump ya bayyana cewa, a halin yanzu ƙarfin sojin Iran ya ragu matuƙa, yana mai cewa yawancin manyan kayan yaƙinsu sun lalace, inda ya yi zargin cewa ƙasar ta rasa manyan hanyoyin sadarwar soja da wasu muhimman kayan yaƙi.

By Babaji