Gwamnatin Tarayya ta san suna da wajen da kowane ɗan ta’adda yake, inji Sheikh Gumi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen Malamin addinin Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta san sunayen dukkan ‘yan ta’addan da ke addabar ƙasar tare da wuraren da suke ɓoye kansu.

Gumi ya ce bayanan da hukumomin tsaro ke da su sun isa su gano kowane dan ta’adda, domin a cewarsa, “sun san su da suna, sun san inda suke zaune, tare da wuraren da suke gudanar da ayyukansu.”

Ya bayyana cewa abin da ake bukata yanzu shi ne daukar matakai masu ƙarfi da kuma amfani da dabaru na musamman domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta jima tana addabar sassa da dama na ƙasar.

Ya kara da cewa, idan aka haɗa ƙarfi da karfe tsakanin gwamnati, jami’an tsaro da kuma al’umma, za a iya kawo karshen ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga a kasar cikin kankanin lokaci.

Ya kuma jaddada matsayarsa ta cewa tattaunawar sulhu ita ce ta hanyar da ta fi dadewa da magance matsalolin rikice-rikice da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.

By Babaji