Matatar Warri tana aiki da kashi 60 cikin 100 ne, inji Kyari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matatar mai ta Warri mai ƙarfin tace ɗanyen mai ganga 125,000 a kowace rana ta dawo aiki da ƙarfin tace mai kashi 60 cikin 100.

Wannan ya fito ne ta bakin babban jami’in rukunin kamfanin na Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari yayin rangaɗin da ya kai matatar a ranar Litinin.

Hakan ya nuna cewa kashi 60 cikin 100 na ganga 125,000 da ake haƙowa a kowace rana ya ragu zuwa ganga 75,000 na fanyen mai a kowace rana da matatar ke sarrafawa.

Kafin a fara rangaɗi a matarar, an ga Kyari yana jawabi ga tawagar, yana mai cewa “Muna da buri a kan ku. Duk da cewa ba a kammala kashi 100 busa 100 ba, har yanzu muna kan aikin. Mutane da yawa suna tunanin waɗannan abubuwa ba gaskiya ba ne. Suna ganin abubuwa na gaske ba su yiwuwa a ƙasar nan. Muna son ku tabbatar musu da gaskiya ne.

“Dole ne in taya tawagarmu murna saboda jajircewarsu ganin cewa wannan matatar ta sake fara aiki.

“Wannan ya kawo sakamakon da muke gani tare da haɗin gwiwar ‘yan kwangilar mu. Mun tabbatar da cewa yana yiwuwa a sake kunna matatar da aka rufe da gangan.

“Wannan matata tana da matakai uku. Mun fara mataki na ɗaya wanda ake kira Area 1, mai iya samar da dizal, kalanzir, da sauransu. Waɗannan samfura ne masu inganci da ake buƙata a cikin ƙasa. Za mu kuma iya fitar da su waje. Wannan ƙasa za ta samu kuɗi don cika alƙawuran da shugaban ƙasa ya ɗauka.

“Dole ne in bayyana cewa ci gaban ya kasance ne sakamakon buƙatar da shugaban ƙasa ya yi cewa dole ne mu sa matatun guda uku su yi aiki, wanda aka riga aka fara. Mun samu nasarar fara aikin matatar mai na Fatakwal da tace ganga 65,000 a kowace rana. Haka kuma mun ƙaddamar da yankin area 1 na matatar mai na Warri. Sauran ɓangaren matatar da za su samar da man fetur daga baya.

“Matatar Kaduna ma tana kan hanya. Ba za mu ba ku kwanan wata ba amma za mu ba ku tabbaci.”

Cikin tawagar da suka kai ziyarar har da babban jami’in hukumar kula da harkokin tacewa da haƙo man fetur ta Nijeriya (NMDPRA), Farouk Ahmed.

By ukarofi