Matawalle: Ƙungiyar manema labarai ta Arewa ta nemi a hana cin mutuncin ƴan jarida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar manema labarai ta Arewa ta nuna damuwa kan yadda wata Babbar Kotun Tarayya dake ƙaramar hukumar Bichi a Jihar Kano ta ci mutuncin wasu ƴan jarida.

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya shigar da ƙara kan wasu shahararrun ƴan jarida biyu, Shua’ibu Mungadi na gidan rediyon Vision da Ahmed Tijjani Ramalan na gidan rediyon da telebijin na Freedom wanda hakan ya ci karo da sashi na 22 na kundin dokokin ƙasa da ya bai wa ƴan jarida damar bibiyar ayyukan masu muƙaman gwamnati da kuma sashi 39 da ya bada damar yin jawabi.

A cikin wata takarda da shugaban ƙungiyar, Abdullahi Yelwa ya fitar, ƙungiyar ta nuna damuwa game da yunƙurin ministan wanda ta ce hakan wani nau’i ne na ƙoƙarin hana ƴan jarida yin ayyukansu bisa ƙwarewa.

Ya ce, sun yi mamakin yadda Matawalle ya ware waɗannan manyan ƴan jaridar da ake girmama su game da matsalar da al’umma suka jima suna tattauna ta.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana hakan a matsayin wani yunƙuri na hana ƴancin aikin jarida da kuma toshe duk wata kafa da za ta fallasa zargin rashawa da ake masa a lokacin da ya ke gwamna a Jihar Zamfara.

Ƙungiyar ta yi kira ga Majalisar kula da alƙalai (NJC) da Antoni Janar na Ƙasa da su binciki lamarin da kuma halin da ke sa kotun ta umarci a dakatar da ƴan jarida.

Haka kuma su yi nazari game da ƙarar da aka shigar akan ƴan jaridun da zargin saɓa ƙa’ida da kuma tabbatar da adalci kan dokokin aikin jarida.

Har’ilayau ƙungiyar ta nemi Ministan Labarai da Wayar da kan Al’umma da ya tsoma baki cikin lamarin don dakatar da tauye haƙƙi ko cin mutuncin ƴan jaridu.

Kazalika, ya ce a matsayinsu na masu aikin jarida da mallakar gidajen jaridu za su cigaba da yin ayyukansu bisa ƙwarewa da kuma yadda doka ta tsara.

By Babaji