Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gogarman ‘yan bindiga Bello Turji ya bayyana yadda ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya ƙara wa ‘yan bindiga ƙarfin kai hare-hare daga cikin gari a lokacin da ya ke gwamna a Jihar Zamfara.
Lokacin da Bello Matawalle ke gwamna tsakanin 2019 zuwa 2023, ya bijiro da shirin yi wa ‘yan bindiga afuwa, inda ya riƙa bada kuɗaɗe da kariya ga ‘yan bindigar da suka damƙa wa hukuma makamansu, su ka daina ta’addanci.
To sai dai kuma Turji ya ce wannan shirin afuwa bai yi nasara ba, sai ma ƙarfafa wasu abokan sa ‘yan bindiga ɗin ya yi, waɗanda a cewarsa yanzu suna cikin garuruwa inda daga can suke jagorantar gungu-gungun ‘yan bindiga da ke cikin daji.
Turji ya bayyana haka a cikin wani bidiyon da aka watsa a ranar 18 ga Yuli, inda a ciki aka nuno shi tsaye tare da wasu gogarmomin ‘yan bindiga tsaye da muggan makamai.
Ya ce ‘yan bindigar da aka yi sulhu da su aka yi masu afuwa a lokacin mulkin Bello Matawalle, ai ba su yi sarandar makamansu duka ba. Maimakon haka, sai suka ci gaba da kai hare-hare ta hannun yaransu dake cikin daji.
Turji ya ci gaba da yin zargin cewa tsarin afuwa ga ‘yan bindiga a zamanin tsohon gwamnan shi ne dalilin ƙara ruruwar fitinar wutar matsalar tsaro a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.
Turji ya ƙara da cewa shi da kan sa ya kashe wani ɗan bindiga kuma gogarma a ƙaramar Hukumar Shinkafi, domin a samu zaman lafiya.
Amma daga baya sai aka yi zargin gwamna ne ya yi wa ƙoƙarin da shi Turji ɗin ya fara yi zagon ƙasa.
“Duk mutumin da ke zaune a Shinkafi, Zurmi da Isa ba za su ƙaryata ni ba. Akwai gungun wasu ‘yan bindiga waɗanda tsohon gwamna ya riƙa bai wa kuɗaɗe. Ni na kore su daga yankin Shinkafi. Ni na kashe shugabansu Dudu domin a samu zaman lafiya a yankin Shinkafi.
“Su na da bindigogi sun kai 200, amma gwamnan ya karɓi yaran Dudu a Gidan Gwamnatin Zamfara. Amma kuma gwamna ya ƙi cewa su bayar da bindigogin su. Sai kuma wani gungun da gogarma Bashari Maniya, masu bindigogi sama da 300. Ni na ƙwace bindigogi 30 daga hannun su. Shin yanzu ina sauran bindigogin? Babu wata rana ɗaya da suka yi sarandar bindigogin ga gwamnati,” cewar Turji.
Ya ƙara cewa wasu shugabannin ‘yan bindigar da Matawalle ya yi sulhu da su sai suka koma cikin garin Sakkwato, suka bai wa yaran su da ke cikin daji, suka riƙa yin garkuwa da mutane ana biyan su kuɗaɗen fansa. Ya ce yaran duk lokacin da suka karɓi kuɗaɗen fansa, su na aika wa shugabannin su da ke cikin Sakkwato na su kason.
Ya lissafa wasu daga cikinsu da suka haɗa da Bashari Maniya, Kabiru da Buhari.
“Ɗan Maigari ƙanin Bashari Maniya ne; ya na da bindigogi sun kai 150, kuma a cikin dajin Maradun yake ɓoye, shi ne ke kai hare-haren da ake kaiwa a yankunan Maradun.
“Ali kuma yaron Kabiru Mabiya ne, shi ne gogarman kai hare-hare a yankin Tangaza. Bashari da Kabiru kuma a Sakkwato suke zaune, su na jin daɗin su. Akwai wani kuma Buhari, shi ma yana cikin Sakkwato zaune ya na jin daɗin sa.
“Makonni uku da suka gabata, wani Ƙanin Buhari an kama shi da bindigogi a cikin garin Sakkwato. A samu wani ya fito ya ƙaryata ni. Zan iya kawo bidiyon sa da Kabiru, inda aka ga Kabiru na harba mashinga.
“Tambaya a yanzu ita ce, ina mashinga-mashinga ɗin bayan sun ce sun karɓi tayin sulhu wai sun tuba, su na zaune a Sakkwato? Wa ya damƙa wa mashinga ɗin? Ya kamata gwamnati ta yi wa ‘yan Nijeriya bayanin su wane ne ke ta kashe mutane? Su daina ɗora laifi ga Bello Turji wai ya na kisan mutane ya na garkuwa.
“Mutanen da ake ɗauka daga cikin garin Sakkwato ana kai su bayan Achida da Goronyo, shin su wane ne ke wannan garkuwa da mutanen. Shin su ma Bello Turji ɗin ne? Wa ke zaune lafiya a Shinkafi?” Tambayar Turji.
Manhaja ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Ministan Tsaro Bello Matawalle, amma lambar wayar Kakakin Yaɗa Labaransa, Ahmad ɗan-Wudil ta ƙi shiga.
