Matsalar warin baki da hanyoyin magance ta (2)

Daga BILKISU YUSUF ALI

Ci gaba daga makon da ya gabata

Duk da warin baki ba za a kira shi da gama-garin matsala ba amma mutane da yawa na fama da shi kuma matsala ce da ake iya jin ta daga nesa kafin ma a kusanci mutum.

*Babbar matsala ta farko da ke janyo warin baki shi ne rashin tsaftar baki , in kuwa haka ne maganin farko na wannan matsalar shi ne tsaftace baki da duk nau’ikan abin da aka tanada don tsaftace baki.

*Ganin likitan haƙori duk lokacin da aka fuskanta akwai matsala ta ciwon haƙori ko dasashi, don sau tari haƙori ne kan lalace ko ya yi kogo sai yake tara datti a ciki. Haka ciwon haƙori kan janyo warin baki. Wanke baki akai akai musamman duk lokacin da aka ci abinci a ƙalla ko da ruwa ne a kurkure bakin a tabbatar wani abu bai maƙale ba, sannan a lokacin kwanciya bacci a tabbatar an wanke baki da man goge baki ko gawayi da gishiri ko kuma asiwaki.

*Kuskura baki da ruwan Khalli Tuffa da ruwan kanumfari yana taimakawa wajen magance warin baki kwarai da gaske ana tafasa su a ruwa a ke kuskure baki da su bayan an ɗan bar su lokaci kaɗan a cikin baki a yi haka kullum sau uku a rana. In sha Allah za a samu waraka.

*Tauna Kanumfari yana magance larurorin haƙori da warin baki.

*Yawan shan ruwa yana taimakawa wajen hana bushewar baki da ƙafewar yawu.

*Cin cingam marar zaƙi kan sa baki ya zama wasai kuma yana sa jijiyoyin baki su samu motsuwa kuma yana hana warin baki.

•Ga mai larurar warin baki yana da kyau ya dimanci kuskure bakinsa da ruwan ɗimi da gishiri kaɗan a ƙalla sau uku a rana ko ma fiye. Yin hakan na kashe kwayoyin cutoci da suke baki sannan kuma yana tsaftace baki ya sa shi ya yi wasai.

•Akwai tsari da masana lafiyar baki suka ware wajen goge baki da salon da ake yi shi ma a nemi saninsa yana da muhimmanci sannan kuma a kula da wanke harshe da dasashi yayin wanke baki.

•Yin sakace abinci musamman ga waɗanda abinci kan maƙale musu a tsakankanin haƙora.

•Akwai ganyen Parsly ana haɗa shi da ganyen na’a –na’a a taunasu ko a dandaƙasu a tauna a ɗan bar shi a baki minti ɗaya zuwa biyu. Ana kuma iya cinsu bayan kowanne cin abinci ɗan kaɗan.

•Warin baki da ciwon sanyi ya haddasa shi sai an magance ciwon sanyin tukunna kafin a tunkari matsalar warin bakin kuma sau ma tari da an rabu da ciwon sanyin sai larurar warin bakin ta gushe.

•Cin ‘ya’yan itatuwa musamman abarba yana magance warin baki.

Amma babbar hanyar magance warin baki bayan tsaftace baki shi ne neman shawarar masana musamman idan an gwada dukkan waɗannan hanyoyi ba a dace ba saboda akwai warin baki da wasu cutoci ne na daban ke haddasa shi

Ga mai neman ƙarin bayani ya turo saƙon tes a wannan layin ko kuma ta WhatsApp; 08039475191 ko a duba shafin Facebook ɗina mai suna Ilham Special Care and Treatment.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *