Nijeriya ta jaddada sadaukarwa ga yarjejeniyar magance bala’o’i ta Sendai a taron COP26

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ta nanata ƙudirin ta na aiwatar da tsarin rage aukuwar bala’o’i wanda aka yi a Sendai domin aiwatarwa daga 2015-2021.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a lokacin da ake tattaunawa kan tsarin da Nijeriya ta ke bi wajen amfani da sauyin yanayi don rage aukuwar bala’o’i a taron duniya kan sauyin yanayi, wato COP26, wanda aka yi a ranar Litinin a birnin Glasgow na ƙasar Sukotland.

A jawabin da ta gabatar kan ƙoƙarin Nijeriya wajen magance matsalolin rayuwa da sauyawar yanayi ke haifarwa, a wani ƙaramin taro da aka yi a gefen babban taron, Hajiya Sadiya ta bayyana halin da ake ciki a Nijeriya a yanzu domin kawo ƙarshen tsaka mai wuya da ‘yan Nijeriya su ke ciki da kuma ƙoƙarin da ake yi wajen yayata buƙatar canjin rayuwa don a tafi daidai da sauyin yanayi kuma a ƙarfafa wa al’ummomi.

Ta ce, “Wajen magance ambaliyar ruwa, yanzu mu na amfani da wani tsarin kula da ambaliya na bai-ɗaya, inda mu ke fahimtar inda ake da matsaloli tare da kautar da ruwan ambaliya zuwa inda za a yi amfani da shi a yi noman rani da kuma samar da wutar lantarki.

“Ta hanyar haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki da su ka kamata, wannan Ma’aikata ta fito da tsarin shirya wa aikin agajin ambaliya na ƙasa, wato ‘National Flood Emergency Preparedness and Response Plan’.

“Manufar tsarin ita ce a samar da bayanan da su ka dace sannan a fito da tsare-tsaren kai agaji don hukumomi da ma’aikatun gwamnati su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da juna idan babban bala’in ambaliya ya auku.

“Ana bada muhimmanci sosai ga batun rage haɗari da kuma rigakafi da hanyoyin rage raɗaɗin aukuwar bala’i, sannan da zaran tsarin ya fara aiki to za a fi saka jama’ar yanki a cikin aikin gudanarwar ambaliya: kama daga bin umarnin gargaɗin farko da hasashen zuwan ambaliya, har zuwa samar da hanya mafi dacewa.

“Tilas ne a tunkari waɗannan matsaloli na sauyawar yanayi domin kuwa a kullum ƙaruwa su ke yi, su na zama manyan bala’o’i da su ka shafi aikin agaji, ba ma a Nijeriya kaɗai ba har ma a dukkan duniya.

“Saboda haka, Ma’aikatar Harkokin Agaji da hukumomin da ke ƙarƙashin ta da abokan aikin ta su na aiki da dabarun kula da sauyawar yanayi tare da aiwatar da bincike kan inda za a iya samun matsala domin a rage haɗarin faruwar lamarin.

“A matsayin mu na masu ruwa da tsaki a wannan tsere, tilas ne mu kawo hanyoyin rage faɗawa cikin haɗari, tsare-tsaren kare jama’a da hanyoyin kai agaji don kare mutanen da za su fi faɗawa cikin bala’i wanda sauyin yanayi ke haifarwa.”

Ministar ta kuma lura da cewa Nijeriya ta na fuskantar ƙarin al’amuran da su ka danganci ruwa kamar su ambaliya, hadari mai ƙarfin iska, fari, zaizayar ƙasa a bakin teku da cikin jihohi, da sauran su, waɗanda su ka jawo babbar asarar dukiya da mace-macen da za a iya kauce mawa.

“Yadda ake yin ruwan sama ya sauya kuma mu na ganin yadda ƙauyuka a ƙananan hukumomi su ke ƙara shiga haɗari tare da faɗawa cikin matsalar ambaliya.

“Ta hanyar hukumar NEMA, mu na kuma aiwatar da ayyukan kula da sauyin yanayi a bisa matakan jiha da ƙauyuka.

“Haka kuma mu na zurfafa bincike da ilimi ta hanyar jami’o’i a Nijeriya.

“Wasu abubuwa da aka yi masu tasiri su ne wayar da kan mutane da kuma rahotannin da NEMA ta tattara ta hanyar tsarin tattara bayanai da ma sa ido tare da bada rahoto da ake yi kan sauyin yanayi da sauran haɗurra.

“Kwanan nan mu ka kammala nazarin haɗari da inda za a iya samun matsala a Nijeriya a ɓangarori uku da aka fi samun haɗurra, wato ambaliya, cututtuka da rikice-rikice.

“Waɗannan bincike-bincike za su taimaka mana wajen fito da dabara tare da inganta tsare-tsaren kula da sauyin yanayi a wuraren da aka binciko.

“Don aiwatar da wannan, mu na gina hulɗoɗi da ƙarfafa hukumomin yaƙi da faruwar bala’o’i a matakin jiha da na ƙaramar hukuma don aiwatarwa da ɗauka.

“Ina so in yi amfani da wannan dama domin in nanata sadaukarwar Nijeriya ga aiwatar da ƙudirin rage aukuwar bala’o’i na Sendai tare da gode wa UNFCCC da Ma’aikatar Kula da Yanayi da su ka kawo wannan batu a taron COP26.”

A wajen ƙaramin taron dai an samu halartar Mista Manuel Marques Pereira, Shugaban Ƙungiyar Sauya Wurin Zama, Muhalli, da Sauyin Yanayi ta Duniya, da Sanata Hassan Muhammed Gusau, Shugaban Kwamitin Yanayi a Majalisar Dattawa, da Mista Vincent Owan, Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Hasashe wanda ya wakilci Darakta-Janar na NEMA, wato Mustapha Habib Ahmed, da Darakta-Janar na NIHSA, Injiniya Clement Eze.