Matsalolin haƙora da yadda za a magance su

Daga AISHA ASAS

Ciwon haƙora na ɗaya daga cikin curuta mafi ɗaukar hankalin mai tare da su, kuma ciwon ya zama ruwan dare a tsakanin mutane, wataƙila hakan ba ya rasa alaƙa da rashin sanin hanyoyin da ke iya haddasa matsala a haƙoran namu na daga hanyoyin kula da su.

Akwai ɗabi’u da dama da muka maida ba komai ba, amma sukan zama silar kamuwa da wata nau’in cutar haƙora. Darasin namu na wannan sati zai karkata ne kan matsalolin da kuma yadda za a iya magance su, don haka ba za mu samu damar nutsewa cikin bayanin yadda muke cin karo da matsalolin haqoran da ɗabi’un da ke zama silar samuwar su ba. Wannan darasi ne mai zaman kansa da muke fatan kawo wa masu karatu shi nan da bada jimawa ba.

Matsalolin haƙora suna da yawa, kuma hanyoyin maganinsu ma haka, don haka za mu yi amfani da ɗaya daga cikin ni’imar da Allah Ya yi mana ta ɓangaren tsiro, wato tumfafiya.

Idan ki na cikin masu fama da matsalar haƙora mai sa matsanancin ciwo na haqoran, to ki nemi itacen ita wannan itaciya a dafa tare da ɗan gishiri, jar kanwa da kuma ɗan kanunfari.

Idan ya ɗan huce, (kada a bari ya huce gabaɗaya, hucewa yadda baki zai iya amsar sa ba tare da ya ƙone ba). Za a dinga cika baki da shi, tsayin mintuna uku, sannan a zubar. Ana maimaita hakan safe da dare.

Haka ma ta vangaren mai fama da matsalar Kogon haƙora, idan har mai karatu masani je kan itaciyyar ta tumfafiya, ya san akwai kaɗa cikin ƙwallon tumfafiya, sannan ana samun wani ruwa mai kalar madara yayin da aka cire ƙwallon.

Waɗannan ababe biyu ne muke buƙata yayin samar da wannan maganin. Za a ɗauki kaɗar ne, a dangwali ita wannan madarar, sai a sanya a daidai inda kogon yake. Za a aikata hakan sau ɗaya a rana. In sha Allahu za a wayi gari an magance wannan matsala.