‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama a Kaduna

*Gwamna El-Rufai ya yi tir da kisan

Sojoji sun ce ‘yan bindiga sun halaka mutane da dama tare da jikkata wasu a ƙauyen Runji da ke cikin yankin Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Jihar Kaduna.

Bayanan sojojin sun ce an kai harin ne ranar Asabar da daddare.

Rahotanni farko da sojojin suka fitar sun nuna an ƙona gidajen da ba a tantace adadinsu ba a ƙauyen.

Sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harakokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan, ya fitar ta ce rahoton sojojin ya ce an yi ɗauki ba daɗi tsakanin jami’an tsaro da maharan.

Rahoton ya ƙara da cewa, har yanzu akwai maharan a warwatse a sassan yankin.

Da safiyar Lahadi Gwamna Nasir El-Rufai ya karɓi rahoton harin tare da bayyana harin a matsayin abin damuwa.

Gwamnan ya jajanta wa waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a harin tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *