Rikicin siyasa ya ci mutum uku a Kano

Ana fargabar mutum uku sun mutu sakamakon rikicin zaɓe da ya ɓarke a yankin Ƙaramar Hukumar Wudil a Jihar Kano.

Jaridar News Point Nigeria ta ce wasu ‘yan daban siyasa ne suka kai hari rumfar zaɓe a yankin wanda hakan ya haifar da rikici yayin zaɓen na ranar Asabar da ta gabata.

A cewar wani wanda lamarin ya faru a gabansa, rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku tare da ƙona gidaje aƙalla guda uku.

Sai dai kuma, da aka nemi jin ta bakinsa Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, Haruna Kiyawa, bai tabbatar da faruwar hakan ba.

Ya ce zai iya ba da bayani kan adadin waɗanda suka mutu ne bayan ya samu cikakken bayani daga Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Ibrahim Sani Koeje, da ke lura da zaɓen.

Tuni dai Koeje ya kai ziyara yankunan da lamarin ya shafa, wato kauyukan Darki, Achika da Utai don gane wa idanunsa abin da ya auku.