Sakkwato ta Arewa: Sanata Wamakko ya yi ta-zarce

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko na Jam’iyyar APC ya sake lashe zaɓen sanatan Sakkwato ta Arewa.

Wamakko ya samu nasarar ce a zaɓen cike giɓin da INEC ta gudanar a ranar Asabar inda ya samu ƙuri’u 141,468.

Abokin hamayyarsa na Jam’iyyar PDP, Dan’iya Manir Muhammad ne ya zama na biyu da ƙuri’a 118,445.

Farfesa Ibrahim Magawata shi ne Baturen Zaɓen da ya bayyana sakamakon zaɓen da aka gudanar a rumfunan zaɓe 185.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *