Mece ce alaƙar Tinubu da matatar mai ta Malta?

Spread the love

Daga ALIYU SAMBA

Al’ada ce ta kafafen sada zumunta a duk sanda mutane suka karkata ƙarfin su akan wani lamari, za a yi ta samun fitowar bayanai da ko dai su tunzura mutane, ko kuma su fahimtar da su, a wannan yanayin kuma a kan samu labarai na gaskiya da kuma na jabu da ake yaɗawa don cimma wani hadafi, mutane kuma suyi ta yaɗawa bisa sani da rashin sani.

Kamar haka ne yanzu yake faruwa a daidai lokacin da wasu suka fake da yanayin da ƴan ƙasa ke ciki na tsanani sakamakon riƙon sakainar kashi da gwamnatocin baya sukai wa ƙasar, suke kuma tunzura matasa don su samu damar cimma nasu hadafin. Ganin babu nasara a wancan fagen ya sa suka sauya linzami zuwa sabon batun mallakar rijiyoyin mai ga Tinubu.

Tabbas kamar yadda masu yaɗa wancan farfagandar ke faɗa, an sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin kamfanin Oando da Agip a ranar 4 ga watan Satumba, 2023. Saidai, yarjejeniyar ba ta kai bantenta ba sai a kwanan nan, sakamakon buƙatar wasu matakai da tsare-tsare na wajibi da ba a kammala cikawa ba. Za a gudanar da bikin sanya hannu kan tabbatar yarjejeniyar nan ba da jimawa ba.

Wasu mutane na son amfani da wannan bidiyo na Ɗan Bello da kuma rubuce-rubuce da ake yi don tabbatar da cewa a yanzu dukkan ragamar hada-hadar ɗanyen mai da shigo da tataccen mai na hannun kamfanin Oando, saidai kuma sun manta cewa har yanzu ma ba ta inda kamfanin Oando ke da cikakken iko akan gudanarwar kamfanin na Agip da kuma abubuwan da ya samar a shekarar 2023.

Ya kamata mai karatu ya karanta wannan gaɓar da kyau, kamfanin Oando ya na samun ganga Miliyan 11 na ɗanyen mai a shekara daga Najeriya, ta yaya kenan zai zama kamfanin ke tace dukkan man Najeriya da ke samar da ganga Miliyan 552.84 a kowacce shekara? A kowacce rana, Najeriya na samar da ganga Miliyan 1.51 na ɗanyen mai, idan aka dauki wancan lissafin na ganga miliyan 11 a shekara na Kamfanin Oando, zai zama ganga 30,000 kamfanin ke samu a kullum. Ta yaya wanda ke samun ganga 30,000 cikin ganga Miliyan 1.51 ke riƙe da ragamar hada-hadar man ƙasar nan?

In a na magana akan kamfanoni da ke hada-hadar ɗanyen mai a ƙasar nan, kamfanin Agip baya cikin manyan kamfanoni goman farko na ƙasar nan. Manya kamfanoni biyar na farko sune; kamfanin Mobil da ke samun ganga miliyan 58; NPDC wadda yanzu ake kira NNPCL E&P ke samun ganga miliyan 50.5; sai kamfanin SNEPCO da kuma SPDC dake samun ganga miliyan 45; sai CHEVRON dake da ganga miliyan 38; sai na biyar, kamfanin Total E&P mai ganga miliyan 38. Kamfanin Nigeria Agip ya samu ganga miliyan 5.7 ne a shekarar 2023, ta yaya kenan yarjejeniyar su da kamfanin Oando zai sa Oando riƙe ragamar haƙo mai a Najeriya?

Mu dawo maganar fitar da ɗanyen mai zuwa kasashen waje da ake son nuna wa ƴan Najeriya cewa garin da bai kai girman Legas ne ke tace man da ake kawowa Najeriya. Ƙasashe 5 da aka fi kai man Najeriya a duniya bisa rahoton watanni 4 na farkon wannan shekarar ta 2024 sune; Faransa, Isfaniya, Netherland, Indiya da kuma Amurka wanda mafi yawan abinda ake fitarwa shine danyen mai da kuma ‘Natural Gas’. Malta bata cikin wurare 10 da aka fi fitar da ɗanyen man Najeriya.

Wannan na ƙaryata masu yaɗa cewa Shugaba Tinubu na amfani da ikonsa wajen fitar da man Najeriya zuwa Malta don a tace shi ko kuma a ɓoye, kamar yadda ake ta yaɗawa dan shafawa gwamnatin baƙin fenti.

Sa’annan, ko da ma kamfanin Malta mallakin Tinubu ne, kamfanin na samar da kaso 11 ne cikin 100 na tataccen man da ake shigo da shi zuwa kasar nan. Akwai kaso 89 da ke shigowa daga wasu wuraren. Ta yaya mai shigo da kaso 11 cikin 100 zai zama shine ke kwashe dukkan kuɗin da aka ware na tallafin mai na Najeriya?

Ba na mamaki idan na ga ana amfani da irin wannan ‘Cheap Propaganda’ don aibanta gwamnati, amma tun bayan lalacewar matatun mai mallakin gwamnatin Najeriya, ba a yi wata gwamnati dake hoɓɓasa da ƙoƙarin farfaɗo da su ba kamar wannan gwamnatin, kuma muna da kyakkyawan fatan cewa nan da shekara mai zuwa matatun man mu zasu fara aiki, wanda hakan zai taimaka wajen rage fita mai zuwa ƙasashen ƙetare a tace ma na mu siya, kuma sai a rage farashin mai a faɗin kasar.

By Babaji