Daga RABI’U SANUSI
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara sassauta dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe shidda na safiya zuwa shidda na Yamma.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne na Jihar Kano ya bayyana haka a taron majalisar zartawa dake gudana yanzu a fadar gwamnatin Kano.
Gwamna Abba Kabir ya ce wannan ya biyo bayan taron majalisar tsaro da ya gudana yau ɗin nan kafin fara taron majalisar ta zartarwa da yake gudanar.
